Ido ya raina fata: An gurfanar da wasu yan mata biyu a kotu, bayan lakadawa Dan sanda duka tare da yaga masa kayansa

Ido ya raina fata: An gurfanar da wasu yan mata biyu a kotu, bayan lakadawa Dan sanda duka tare da yaga masa kayansa

- Wasu yan mata biyu sun sha tafi karfin cikinsu, bayan duka tare da yaga kayan Dan sanda da su kayi

- Yanzu haka dai suna fuskantar kwana a gidan kurkuku mutukar ba su cika sharrudan belin su ba

Idanun wasu yan Mata yaya da kanwa masu suna Favour Ajula da Oluchi Ajula ya raina fata, sakamakon taron dangi wajen lakadawa jami'in Dan sanda dukan tsiya tare da kuma yayyaga masa kakinsa da kuma yunkurin kwace bindigarsa da su kayi.

Yan sanda dai sun gurfanar da yan matan biyu ne gaban mai shari'a F.F. George yau Alhamis, inda ake tuhumarsu da laifuka biyu; tuggu (sharri) da kuma hadinkai da cin zarafin jami'in rundunar yan sanda mai mukamin sufeto.

Ido ya raina fata: an gurfanar da wasu yan mata biyu a kotu, bayan lakadawa Dan sanda duka tare da yaga masa kayansa

Ido ya raina fata: an gurfanar da wasu yan mata biyu a kotu, bayan lakadawa Dan sanda duka tare da yaga masa kayansa

Babbar mai suna Favour na da shekaru 24, yayinda Oluchi kuma ke da shekaru 18. dukkanninsu mazauna unguwar Iju-Ishaga dake Agege a jihar Lagos.

KU KARANTA: Duba Wurare hudu da Trump da Buhari suka yi kamanceceniya da juna Author: Muhammad Mubarak Bala

Dan sanda mai gabatar da kara Sgt. Godwin Awase, ya shaidawa kotu cewa, sun karbi korafin wani da suke zaune gidan haya tare da yan matan mai suna Uche Prince, kan cewa sun yi barazanar kashe shi.

Wannan ta sa jami'in Dan sandan mai suna Sufeto Bitrus Zingkur ya bi shi domin jin ba'asi da kuma sasantwa, da isar su gidan shi ne suka yi taron dangi suka yi ta jibgarsa tare da yunkurin kwace bindigarsa wai kawai don ya nemi sasanta su.

A cewar Dan sanda mai gabatar da kara yin hakan, karan tsaye ne ga sashi na 174(b) da na 411 na kudin dokar manyan laifuka ta jihar Lagos na 2015.

Sai dai kuma wadanda ake karar sun musunta wannan zargin, dagan nan ne alkali ya ba da su beli kan kudi Naira N50,000 kowannensu sannan kuma dole ne su kawo wandanda zasu tsaya musu, kana kuma mai shari'ar ya ce, masu karbar belin nasu su zamto kowannensu na da aiki da kuma takardar shaidar biyan haraji na shekaru biyu.

Daga nan ne kuma alkalin ya dage shari'ar zuwa ranar 14 ga watan Mayu domin cigaba da shari'a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel