Sojoji sun tare Boko Haram daga kai hari a Borno

Sojoji sun tare Boko Haram daga kai hari a Borno

- Hukumar ‘Yan Sanda a jihar Borno sun bayyana cewa jami’an sojin Najeriya sun tare ‘yan kungiyar Boko Haram lokacin da sukayi yunkurin kaiwa sansanin sojin hari wanda ke kauyen Auno kai hari a karamar hukumar Kaga dake jihar

- Mista Edet Okon jami’in ‘Yan Sanda mai kula da harkokin jama’a yace jaruman sojojin sun tare ‘yan Boko Haram din ne a kusa da sansanin sojoji dake yankin

- Okon ya bayyana cewa ‘yan Boko Haram din sun dan tabawa sojojin mota amma dai babu wata asarar rayuka ko rauni da aka samu

Hukumar ‘Yan Sanda a jihar Borno sun bayyana cewa jami’an sojin Najeriya sun tare ‘yan kungiyar Boko Haram lokacin da sukayi yunkurin kaiwa sansanin sojojin hari wanda ke kauyen Auno kai hari a karamar hukumar Kaga dake jihar.

Mista Edet Okon jami’in ‘Yan Sanda mai kula da harkokin jama’a a garin Maiduguri ya bayyana cewa jaruman sojojin sun tare ‘yan Boko Haram din ne a kusa da sansanin sojoji dake yankin a ranar 2 ga watan Mayu.

Sojoji sun tare Boko Haram daga kai hari a Borno

Sojoji sun tare Boko Haram daga kai hari a Borno

Okon ya bayyana cewa ‘yan Boko Haram din sun dan tabawa sojojin mota amma dai babu wata asarar rayuka ko rauni da aka samu, sakamakon harin da sukayi yunkurin kaiwa a sansanin sojoji dake kusa da kauyen Auno a kan hanyar Maiduguri-Damaturu.

KU KARANTA KUMA: Dan takarar shugaban kasa ya shawarci mata da karda su yarda su tara da mazajensu idan har basu da katin zabe

Okon ya kara da cewa an kara tura jami’an soji da na ‘yan sanda a yankin don kara tabbatar da tsaro a yankin, sannan kwamishinan ‘ya sandan Damian Chukwu, yayi kira ga jama’a dasu cigaba da tafiyar da al’amuransu nay au da kullum ba tare da fargaba ba

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel