EFCC ta gano waso kadarori mallakar wata shugaban banki da ta boye a Dubai

EFCC ta gano waso kadarori mallakar wata shugaban banki da ta boye a Dubai

A kokarinta na binciko dukiya al'umma da aka sace, EFCC ta gano wasu kadarori dake Dubai mallakar tsohuwar Babban Daraktan Bankin Oceanic, Mrs Cecilia Ibru. Dukiyoyin sun hada da shaguna 41 da manyan gidaje 16 da husumiyoyi guda hudu.

Duk da cewa an kwace dukkan kadarorin kuma an sayar da su, kudaden da aka sayar basu shigo assusun gwamnati ba. An sayar da kadarorin ne a kan kudi $4,522,413.20 amma $3,278,238.69 ne kawai ya shiga asusun Hukumar kula da kadororin kasa AMCON.

EFCC ta gano waso kadarori mallakar wata shugaban banki ta boye a Dubai

EFCC ta gano waso kadarori mallakar wata shugaban banki ta boye a Dubai

Cinikayyar sayar da kadarorin ne ya sanya hukumar EFCC tuhumar ma'aikatan AMCON su hudu da kuma tsohon shugaban wajen wanda yanzu haka yana tare da banki.

KU KARANTA: An sake bude makarantar sakandire na 'yan mata da ke Dapchi

An gayyaci ma'aikatan bankuna da dama domin aji yanda akayi kudade suka bar Dubai suka dawo asusun wasu mutane da kamfanoni a Najeriya.

A ranar 9 ga watan October 2019 ne Justice Daniel Abutu na babbar kotun dake Legas ya yankewa Mrs Ibru hukuncin zaman gidan kaso na watanni 18.

Sannan ya bata umarnin maidawa kasar miliyan N191 ta hannun AMCON. Takardar ta bayyana dukiyoyin da ake zargin Mrs Ibru akai wadda ta share watanni Shida a gidan kaso na Dubai.

Takardar ta nuna cewa "Kusan kayayyaiki 61 ne suka bace a hannun Mrs Ibru a Dubai da kuma bayani daga AMCON, 41 daga ciki sun kasance shaguna ne, sai gidaje 16 da kuma husumiyoyi guda Hudu"

EFCC tana kokarin rinjayo Williams akan saida kayan inda ta tura masa goron gayyata amma bai amsa gayyatar ba, duk da cewa ta tabbatar da cewa waskiar gayyatar ta isa gareshi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel