Ina kokarin biyan bashin albashi amma Gwamnonin APC sallamar Ma’aikata su ke yi - Fayose

Ina kokarin biyan bashin albashi amma Gwamnonin APC sallamar Ma’aikata su ke yi - Fayose

- Gwamna Fayose yayi kaca-kaca da Gwamnonin Jam’iyyar APC

- Gwamnan yace gara shi da yake kokarin biyan albashi a Jihar sa

- Wasu Gwamnonin Jam’iyyar APC sun kori Ma’aikatan Jihar su

Mun samu labari cewa Mai Girma Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Peter Fayose yayi kaca-kaca da wasu Gwamnonin Jam’iyyar APC a dalilin korar Ma’aikata da su ke yi da yake magana a shafin sadarwa na zamani a makon nan.

Ina kokarin biyan bashin albashi amma Gwamnonin APC sallamar Ma’aikata su ke yi - Fayose

Gwamna Fayose ya soki Gwamnonin da ke korar Ma'aikata

Gwamna Ayo Fayose wanda shi ne Shugaban Gwamnonin Jam’iyyun adawa na PDP ya bayyana cewa gara ire-iren su Gwamnonin da su ka gaza biyan albashi amma su ke bakin-kokarin biya a maimakon masu korar Ma’aikata.

KU KARANTA: Sojoji sun ceci wata Baiwar Allah a Yankin Boko Haram

Shi dai Gwamnan ya bayyana ra’ayin sa ne a shafin san a Tuwita a jiya cikin dare. Gwamna Ayo Fayose yace wasu Jihohin da APC ke mulki dai ana ta sallamar Ma’aikata ne. Ba dai yau bane Gwamnan ya fara sukar Gwamnatin APC.

A Najeriya dai irin su Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sallami Malaman Makaranta 20000 da kuma sauran Ma’aikata. Shi dai Gwamnan na Ekiti yace yana kokarin biyan makudan albashin da Ma’aikatan Jihar ke bin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel