Har yanzu bana goyon bayan sake takarar Buhari - Obasanjo

Har yanzu bana goyon bayan sake takarar Buhari - Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya nisanta kansa daga ikirarin cewa ya canja matsayarsa akan sake takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Obasanjo ya kuma bayyana cewa shi bai gana da shugabannin kungiyar kwadago ba a ranar Talata kamar yadda akayi zargi.

Obasanjoya jadadda cewa yana nan akan jawabinsa day a saki a watan Janairu na cewa gwamnatin Buhari ta kunyata wadanda suka abe shi a matsayin shugaban kasa.

Har yanzu bana goyon bayan sake takarar Buhari - Obasanjo

Har yanzu bana goyon bayan sake takarar Buhari - Obasanjo

Obasanjo ya bayyana hakan ne a wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinsa, Kehinde Akinyemi shi bai aminta ba kuma ba zai aminta da gajiyayye ba.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa na hana ‘Yan Sanda wulakanta direban adaidaita sahu - Inji wani dan Najeriya

Ya kuma jaddada cewa bai gana da shugabannin kungiyar kwadago ta kasa ba cewa baida gida a Abuja kuma bai je Abuja ba a wannan rana da ake Magana a kai.

A kwanakin baya ne shugaba Buhari ya bayyana kudirinsa na sake takara a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel