Dan takarar shugaban kasa ya shawarci mata da karda su yarda su tara da mazajensu idan har basu da katin zabe

Dan takarar shugaban kasa ya shawarci mata da karda su yarda su tara da mazajensu idan har basu da katin zabe

- Dan takarar shugaban kasa Fela Durotoye a ranar Talata ya bukaci mata dasu hana mazajensu hakkinsu na auratayya idan harbasuyi katin zabe ba

- Durotoye ya bayyana hakan ne a ranar bikin ranar ma’aikata lokacin da yake bayyanawa ‘yan Najeriya dalilin tsayawarsa takarar shugaban kasa

- Durotoye yace ya kamata muyi katin zabe saboda yanada matukar muhimmanci don cigaban rayuwarmu nan gaba

Dan takarar shugaban kasa Fela Durotoye a ranar Talata ya bukaci mata dasu hana mazajensu hakkinsu na auratayya idan harbasuyi katin zabe ba.

Durotoye ya bayyana hakan ne a ranar bikin ranar ma’aikata lokacin da yake bayyanawa ‘yan Najeriya dalilin tsayawarsa takarar shugaban kasan Najeriya ta hanyar kafar sadarwa ta ma’aikatan wadda ake kira ‘The Platform’.

Dan takarar shugaban kasa ya shawarci mata da karda su yarda su tara da mazajensu idan har basu da katin zabe

Dan takarar shugaban kasa ya shawarci mata da karda su yarda su tara da mazajensu idan har basu da katin zabe

Durotoye yace “ya kamata muyi katin zabe saboda yanada matukar muhimmanci don cigaban rayuwarmu nan gaba. Yace a takaice ni a gareni PVC ba wai katin zabe bane kadai, wata izina ce ta zabar wanda raina keso.

KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayinda aka binne jaruma Hauwa Maina

“Na fara wani yunkuri na shawartar ‘yan mata dasu tambayi samarinsu idan sunyi katin zabe, idan har bashi dashi ba sauran soyayya. Sannan kuma ina aiki da wadansu mutane da zasu tabbatar da cewa ko wace matar aure wadda mijinta bashi da katin zabe daga yanzu zuwa watan 1 ga Yuli, ba sauran saduwa tsakaninsu dasu.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel