Ana zargin wani dan shekaru 55 da laifin yi wa yaro dan shekaru 8 fyade a Kano

Ana zargin wani dan shekaru 55 da laifin yi wa yaro dan shekaru 8 fyade a Kano

- Ana tuhumar wani mutum mai shekaru 55 da laifin luwadi da wani yaro dan shekaru 8 a Kano

- Makwabcin iyayen yaron yayi ikirarin cewa wanda ake tuhumar yayi wa yaron dabar ne kuma ya shigar dashi dakinsa

- Sai dai mutumin da ake tuhuma ya musanta zargin da ake masa

A yau Alhamis ne aka gurfanar wani Salisu Muhammad mai shekaru 55 a duniya gaban kotun Majisatare da ke zamanta a birnin Kano inda ake tuhumar sa da aikata luwadi da wani karamin yaro dan shekara takwas.

An kama wani tsoho mai shekaru 55 da laifin lalata dan shekara 8

An kama wani tsoho mai shekaru 55 da laifin lalata dan shekara 8
Source: UGC

Muhammad, mazaunin unguwar Mandawari a Kano yana fuskantar laifin keta hakkin yaron.

KU KARANTA: Majalisar zartarwa ta ware N245bn don gina tituna da wasu muhimman aiki - Fashola

Dan sanda mai shigar da kara, Sufeta Pogu Lale, ya shaidawa kotu cewa wani mutum mai suna Muhammadu Sani wanda ke zaune unguwa daya da wanda ake tuhuma ne ya shigar da kara a caji ofis da ke Mandawari, Kano a ranar 24 ga watan Afrilu.

Ya yi ikirarin cewa a watan Afrilun ne wanda ake tuhumar yayi wa yaron dabara har ya shiga dashi cikin dakinsa.

"Wanda ake tuhumar ya tube wa yaron wanda kuma ya lalata dashi ta duburarsa wanda hakan ya haifar wa yaron rauni."

Mai shigar da karan yace wannan laifin da aka aikata ya ci karo da sashi na 285 na Penal Code.

Sai dai kuma wanda ake tuhuma ya musanta aikata laifin.

Alkalin kotun, Muhammad Jibril ya bayar da belin wanda ake tuhuma kan kudi N50,000 tare da mutane biyu da suka tsaya masa kuma ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 17 ga watan Mayu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel