Halin bera: Budurwa mai tsaron Kanti tayi awon gaba da N894,000

Halin bera: Budurwa mai tsaron Kanti tayi awon gaba da N894,000

- Duk da amincewa da akai mata, wata budurwa ta kalmashe kusan miliyan guda daga shagon da take aiki

- Sai dai kuma wane tudu wane gangare, alkali ya bada belinta

Rundunar yan sanda ta kasa reshen babbar birnin tarayya Abuja, ta gurfanar da wata budurwa mai tsaron kanti bisa zargin sibare makudan kudaden da suka kai N894, 000.

Matashiyar dai mazauniyar unguwar Citec Mbora ce dake kan titin sauka da tashin jiragen sama na Abuja, kuma an gurfanar da ita ne bisa zargin sata a shagon da aka dauke ta aiki a kantin dake Katampe a Abuja.

Halin bera: Budurwa mai tsaron Kanti tayi awon gaba da N894,000

Halin bera: Budurwa mai tsaron Kanti tayi awon gaba da N894,000
Source: Twitter

Dan sanda mai gabatar da kara Zannan Dalhatu, ya bayyanawa kotu cewa, Matar da ta dauke ta aikin ce ta shigar da karar mai suna Zainab Magaji, a ofishin yan sanda dake Utako ranar 27 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Karar kwana: Wani saurayi ya kashe abokinsa a dalilin layin waya

Dalhatu ya ce, wadda ake zargin ta damfari wata mai suna Hafsat Joseph kudi har N894, 000 a shagon wadda ta dauke ta aikin. Sannan ya ce, abinda ta aika laifi ne da ya saba da sashi na 289

na kundin shari'a.

Sai dai kuma bayan zaiyano mata laifin nata, budurwar ta ki amincewa da aikata laifin.

daga nan ne mai shari'a Abubakar Sadiq, ya bayar da belinta kan kudi Naira N500, 000 da kuma wanda zai tsaya mata amma da sharadin yazo da takardar biyan hakkokin da ya kamata duk dan kasa ya biya. kana ya daga shari'ar zuwa 9 ga watan Mayu domin cigaba da sauraron karar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel