Yanzu-yanzu: Kotu ta hana Dino Melaye beli

Yanzu-yanzu: Kotu ta hana Dino Melaye beli

Labaran da ke shigowa yanzu na nuna cewa kotun majistare dake zaune a Lokoja, birnin jihar Kogi inda aka gurfanar da Sanata Dino Melaye da safen nan ta hana shi beli.

Kotun ta bada umurnin cewa sanatan mai wakilttar Kogi ta yamma a majalisan dattawa ya cigaba da kasancewa hannun jami'an yan sandan Najeriya.

An gurfanar da Sanata Dino Melaye ne da safen nan a Lokoja bisa ga laifin baiwa yan baranda makamai da kuma taimakawa wajen arcewansu daga kurkuku.

Alkalin kotun, Cif Majistare Suleiman Abdullahi ya ce sam ba zai bada belin Melaye ba kuma ya umurci hukumar yan sanda su garkame shi har sai ranan 11 ga watan Yuni, 2018.

Yanzu-yanzu: Kotu ta hana Dino Melaye beli

Yanzu-yanzu: Kotu ta hana Dino Melaye beli

A yanzu dai, Sanata Dino Melaye zai kwashe kwanaki 38 a kurkukun yan sanda har sai an cigaba da jin karar a kotu.

KU KARANTA: Buhari ya kulla wata cinikayya da gwamnatin Kasar China da zata rugurguza darajan Dalan Amurka

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa hukumar yan sandan Najeriya ta damke wasu masu garkuwa da mutane kuma sunyi ikirarin cewa Sanata Dino Melaye ne ke daukan nauyinsu.

Duk da cewa sanatan ya musanta wannan abu, hukumar ya ce wajibi ne ya amsa tambaya a gaban kotu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel