Ana cigaba da aikata kisan gilla akan kananan kabilu a Myanmar

Ana cigaba da aikata kisan gilla akan kananan kabilu a Myanmar

- Shugabar kare hakkin dan ta Majalisar Dinkin Duniya wadda ke Myanmar Yanghee Lee ta nuna damuwar ta matuka akan yadda rikici ya barke a jihar Kachin da kuma yadda hukumar sojin kasar ke sakar musu ruwan bama-bamai da kuma aman wuta akan fararen hulan dake yankunan dake makwabtaka da China wadanda basu ji ba basu gani ba

Ana cigaba da aikata kisan gilla akan kananan kabilu a Myanmar

Ana cigaba da aikata kisan gilla akan kananan kabilu a Myanmar

Shugabar kare hakkin dan ta Majalisar Dinkin Duniya wadda ke Myanmar Yanghee Lee ta nuna damuwar ta matuka akan yadda rikici ya barke a jihar Kachin da kuma yadda hukumar sojin kasar ke sakar musu ruwan bama-bamai da kuma aman wuta akan fararen hulan dake yankunan dake makwabtaka da China wadanda basu ji ba basu gani ba.

DUBA WANNAN: Rikicin Benuwe: An kama wani dauke da muggan makamai a jihar Benuwe

A bayanin ta: “Fararen hula wadanda basu ji ba basu gani ba suna ta rasa rayukan su, yayinda hakan ya tilasta wa da yawansu tare da iyalensu yin hijira daga yankin.

Dubun mutanen birnin na Kachin sunyi zanga-zanga a ranar Litinin dinnan domin kira ga hukumar kasar da ta samar da hanya domin kaiwa mazauna wasu kauyukan tallafi wadanda rikicin kananan kabilu da gwamnati ya rutsa dasu.

"Yunkurin kare kai tallafi da dauki ga wadanda ke cikin kakanikayi, ya sabawa dokan kasa da kasa kuma laifin yaki ne inji Yanghee Lee."

Kimanin mutane 4,000 ne aka tilasta su barin garuruwan su domin tsira da rayukan su a jihar ta Kachin dake kusa da kasar China a cikin sati uku da suka gabata. A cikin shekara daya kuwa mutane kimanin dubu 15 ne suka fice daga yankin a yayin da dubu 90 suke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira a jahohin Kachin da Shan tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnati da sojojin Kachin masu zaman kansu a shekarar 2011.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel