Duba Wurare hudu da Trump da Buhari suka yi kamanceceniya da juna

Duba Wurare hudu da Trump da Buhari suka yi kamanceceniya da juna

- Shugaban kasar Amurka Donald Trump dai ya gayyaci shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari zuwa birnin Washington domin su tattauna kan abubuwan da suka shafi kasashen nasu

- A kasa dai zamu kawo muku jerin wuraren da shugabannin biyu suka yi kamanceceniya da juna.

Wurare hudu da Trump da Buhari suka yi kamanceceniya da juna

Wurare hudu da Trump da Buhari suka yi kamanceceniya da juna

Shugaban kasar Amurka Donald Trump dai ya gayyaci shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari zuwa birnin Washington domin su tattauna kan abubuwan da suka shafi kasashen nasu.

Muhammadu Buhari ne ya zamo shugaban Afirka na farko da Mr Trump ya gayyata fadar White House.

A kasa dai zamu kawo muku jerin wuraren da shugabannin biyu suka yi kamanceceniya da juna.

DUBA WANNAN: Rikicin Benuwe: An kama wani dauke da muggan makamai a jihar Benuwe

Ga jerin abubuwan da suka hada shugabannin biyu dai.

1. Duka Sun hau kujerar mulki suna da shekaru fiye da 70 a duniya

Shekarar Shugaban kasa Buhari 73 lokacin da ya hau kujerar mulkin Najeriya a shekarar 2015.

Shi kuwa Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya hau mulkin yana da shekaru 70 a duniya.

2. Nasarar zabensu ya ba kowa mamaki

Shugaba kasa Muhammadu Buhari shi ne dan jam'iyyar hammaya na farko daya samu nasara akan jam'iyya mai ci a tarihin siyasar Najeriya.

Buhari ya samu nasara akan tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan - a tarihin Najeriya ba a taba samun shugaban kasa mai ci da ya sha kaye ba sai shi.

A kasar Amurka kuwa, Hillary Clinton wadda jama'a suka rika hasashen cewa ita ce zata samu nasara a zaben shugabancin kasar.

Sai kuma kwatsam shugaba Trump, wanda hamshakin dan kasuwa ne kuma dan takarar jam'iyyar Republican wato jam'iyyar adawa ta Amurka ya samu nasara, bayan da wasu jihohi da jam'iyyar Democrat take mulki suka zabe shi.

3. Suna samun sabani tsakaninsu da 'yan jarida

Shugaba Donald Trump baya boye rashin gamsuwarsa da 'yan jarida da kuma sauran kafafen yada labarai.

Haka shima shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda tsohon shugaban gwamnatin soji ne, bai cika sakin jiki da 'yan jarida ba musamman na cikin gida Najeriya, shugaban kasar ya fiya bayyana manufofin gwamnatinsa ne a duk lokacin daya yi tafiya zuwa kasashen ketare.

Hakazalika shima ya sha samun matsala tsakanin sa da 'yan jarida ko kafafen sada zumunta, inda yake zargin cewa anyi wa kalamansa mummunar fahimta.

4. An san su da yin katobara

Shugaba Trump mai barota ne a kusan dukkanin sakonnin da yake tura wa a shafinsa na Twitter kuma ana zarginsa da kiran kasashen Afirka wulakanttatu, koda yake shugaban ya musanta zargin da ake yi masa akan cewa yana nuna wariyar launin fata.

Shima Shugaba Buhari ya fuskanci kalubale irin wadannan.

Ya taba maida martani ga kalaman da matarsa tayi inda yace aikinta kawai ta dafa masa abinci kuma a baya-baya nan ya fusata matasan Najeriya inda yace suna jiran gwamnati ta samar musu da komai a kyauta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel