Boko Haram sun kashe mana malaman makaranta 2295 a arewa maso gaba - Ministan Ilimi

Boko Haram sun kashe mana malaman makaranta 2295 a arewa maso gaba - Ministan Ilimi

Ministan Ilimi na kasa, Adamu Adamu, yace kimanin malaman makaranta 2295 ne suka rasa rayyukansu sakamakon hare-haren da 'yan ta'adda ke kaiwa a yankin Arewa maso gabashin Najeriya a shekaru 9 da suka shude.

Ministan ya furta hakan ne a wani taron bita da aka shirya don tattaunawa a kan kudirin dokar samar ta ingantaccen tsaro a makarantu wanda akayi a ranar Laraba a babban birnin taratta a Abuja kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Boko Haram sun kashe mana malaman makaranta 2295 a arewa maso gaba - Ministan Ilimi

Boko Haram sun kashe mana malaman makaranta 2295 a arewa maso gaba - Ministan Ilimi

Ministan ya nuna damuwarsa game da yadda yan ta'addan ke ware makarantun Boko inda ya ce an kashe malaman makaranta guda 2,2295 kuma wasu 19,000 sun rasa muhallin su a jihohin Borno, Yobe da Adamawa a shekaru 9 da suka shude.

DUBA WANNAN: Hatsarin mota dauke da man fetur a garin Zing yayi sanadiyar rasa rayyuka da dukiyoyi

Abinda Ministan ya fada yayi daidai da abinda kungiyar malaman makaranta da gwamnonin jihohin da abin ya shafa suka fadi.

Bayan kashe malaman makarantan, Boko Haram sun kuma kashe a kalla mutane 100,000 tun shekarar 2009 kamar yadda gwamnatin jihar Borno ta bayyana.

Mr. Adamu ya ce 'yan ta'addan Boko Haram din sun lalata a kalla makarantu 1,500 tare da kashe mutane 1,280 wanda suka hada da malamai da dalibai tun shekarar 2014.

A bangarensa, Babban sakataren ma'aikatan Ilimi, Sunny Echono yace akwai bukatar samar da sahihiyar tsarin doka da zai tabbatar da cewa an aiwatar da dukkan tsare-tsaren da aka tanadar don kare makarantun daga harin ta'addanci.

A cewarsa, an kira taron bitar ne saboda a fadakar da masu ruwa da tsaki kan tsarin kiyaye makarantun da kuma yin musayar ra'ayoyi da kasashen da suka aiwatar da dokar kiyaye makarantun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel