Yanzu-yanzu: An iso da Dino Melaye kotun Lokoja

Yanzu-yanzu: An iso da Dino Melaye kotun Lokoja

Labarain da muke samu yanzun nan na nuna cewa jami'an yam sandan Najeriya sun kai Sanata Dino Melaye jihar Lokoja a jiya Laraba.

Da safen nan kuma, sun garzayo da shi kotun majistare da ke Lokoja a kan gadon asibiti domin gurfanar da shi.

Sun kawo shi ne cikin mota kirar Toyota Hiace mai lamba NPF2214D. Ba da dadewa ba za'a gurfanar da shi gaban Alkalin kotu, Ci Majistare Suleiman.

Za'a gurfanar da Sanata Dino Melaye ne kan zargin laifin hada baki da masu garkuwa da mutane, basu kudi da makami, kokarin haddasa fitina a zaben 2019 da kuma taimakawa fursunoni wajen arcewa daga kurkuku.

Tuni Sanatan ya musanta wannan zargi da hukumar yan sanda ke masa amma hakan ba zai isar ba har sai ya bayyana gaban alkalai sun wanke shi.

Yanzu-yanzu: An iso da Dino Melaye kotun Lokoja
Yanzu-yanzu: An iso da Dino Melaye kotun Lokoja

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng