Karar kwana: Wani saurayi ya kashe abokinsa a dalilin layin waya

Karar kwana: Wani saurayi ya kashe abokinsa a dalilin layin waya

- Ganganci ko tsautsayi ya sanya abokai biyu fada wanda hakan ya jawo mutuwar dayan

- Shima wanda yayi kisan yanzu haka yana can ido ya raina fata

Wata kotu a jihar Lagos ta umarci da a tsare wani matashi mai shekaru 32 Seun Efundiya, a gidan kurkuku jiya Laraba a dalilin cakawa abokina kwalba da tayi sandiyyar mutuwarsa.

Rikici ya ɓarke ne tsakanin Efundiya wanda yake sana'ar rijista da kuma sayar da layin waya tsakaninsa da abokin nasa mai suna Ogbe sakamakon aron layi da marigayin ya ce lallai sai ya bashi shi kuma yaƙi.

Karar kwana: Wani saurayi ya kashe abokinsa a dalilin layin waya

Karar kwana: Wani saurayi ya kashe abokinsa a dalilin layin waya

KU KARANTA: Naka shi ke bada kai: An fallasa wadanda suka dasa bam a gidan shugaban Inyamuran Najeriya

Ana cikin wannan sa'insa ne kuma Efundiya ya ɗakko wata fasasshiyar kwalba ya daɓawa Ogbe, nan take ya fara zubar jini wanda hakan yayi sandiyyar mutuwarsa.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN), ya rawaito cewa, wannan aika-aika da mai siyar da layin yayi Efundiya ya saɓasaɓawa kundin tsarin mulki sashi na 223 na manyan laifuka na jihar ta Lagos na 2015, wanda in dai an tabbatar ka iya zama hukuncin kisa ga wanda ake zargin.

Mai shari'a Mrs O.A. Olagbende ya ingiza keyar wanda ake zargin zuwa gidan Maza na Ikoyi kafin yanke hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel