An yi asarar rayuka da dama yayin da makiyaya suka kai mummunan farmaki a jihar Adamawa

An yi asarar rayuka da dama yayin da makiyaya suka kai mummunan farmaki a jihar Adamawa

Wani ibtila’I ya fada ma wasu kauyuka guda uku na karamar hukumar Numan a jihar Adamawa, inda wasu yan bindiga da ake zargin makiyaya ne suka bude ma mutanen kauyukan wuta, tare da banka ma gidaje da dama wuta, kamar yadda gidan Talabijin na ‘Channels’ ta ruwaito.

Kauyukan sun hada ne da kauyen Bolki, Bang da Gon, dukkaninsu a cikin karamar hukumar Numan, shugaban karamar hukumar, Arnold Jibla ya bayyana ma majiyar Legit.ng cewa basu san san adadin mutanen da aka kashe ba.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun kama wani kasurgumin dan bindiga a jihar Benuwe

Rahotanni sun tabbatar da cewar yan bindiga sun far ma kauyukan ne a cikin wata babbar zuga ta yan bindiga a ranar Laraba 2 ga watan Mayu, dauke da muggana makamai, wadanda suka yi amfani dasu wajen hallaka mazauna kauyukan.

Shi ma Kaakakin rundunar Yansandan jihar bai musanta rahoton kai harin ba, amma yace bashi da masaniya. Sai dai al’ummar kauyen Bang dake kan iyakar Adamawa da Taraba sun tabbatar da cewa yan bindigan sun kona kauyen kurmus.

A wani labarin kuma, rundunar Sojojin kasa ta 72 ta cafke wani kasurgumin Dan bindiga dake da hannu cikin kashe kashen da ake yi a jihar Benuwe, Idi Gemu, wanda ta kama shi da bindiga kirar AK 47, sai dai Gemu ya musanta mallakar bindigar, inda yace na abokinsa ne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel