Harin ta'addanci: Majalisar Kasar nan ta sake samun masu hari a kan gine-ginenta

Harin ta'addanci: Majalisar Kasar nan ta sake samun masu hari a kan gine-ginenta

- An kai hari irinsa a baya, an sace sandar majalisa

- Yanzu kuma an sake kai hari majalisar

- Ko ina masu tsaron majalisar suke?

Harin ta'addanci: Majalisar Kasar nan ta sake samun masu hari a kan gine-ginenta

Harin ta'addanci: Majalisar Kasar nan ta sake samun masu hari a kan gine-ginenta

Bai kai sati biyu ba da 'yan ta'adda dauke da makamai suka shiga har cikin majalisar dattawa suka sace sandar majalisar, hargitsi ya tashi a majalisar a ranar laraba saboda bayyanar wasu mutane da makamai, sannan fuskar su a boye wadanda ake tunanin jami'ai ne daga Department of State Service (DSS) suka zagaye harabar majalisar.

Mutane 10 dauke da bindigogi na musamman wadanda ake kira Tavor kuma suka zagaye zaurukan guda biyu na majalisar.

Da aka tambaya mene ne dalilin kawo canjin bazata a yanayin tsaro na majalisar, wani babban jami'in tsaro na majalisar wanda ya bukaci a boye sunan shi, yace an samu wani sabon cigaba ne ta fannin tsarin tsaron majalisar ne.

DUBA WANNAN: Sojin Amurka a Najeriya?

Kamar yanda yace, "Akwai dalilan tsaro wanda bazaku gane ba kuma saboda hatsarinsu baza a bayyana ma mutane ba yanzu."

Wasu daga cikin mutanen an gansu a hanyar shiga majalisar, wasu kuma a hanyar ofishin shugaban majalisar, wasu kuma a hanyar shiga gidan gwamnati.

Majalisar ta gayyaci shugaban 'yan sanda na kasa, Ibrahim Idris don yayi ma majalisar bayyani akan karin tabarbarewar tsaro a kasar inda har yanzu bai bayyana ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel