Ku kalli ayyuka har 109 da shugaba Buhari zai dasa a jihar Zamfara

Ku kalli ayyuka har 109 da shugaba Buhari zai dasa a jihar Zamfara

Shugaba Muhammadu Buhari, mataimakinsa Yemi Osibanjo da gwamnoni da wasu ministoci za su kaddamar da wasu ayyukan biliyoyin naira a jihar Zamfara a yayin da ake bikin cika shekaru 7 na gwamnatin gwamna Abdulaziz Yari.

Shugaban kwamitin shirya bikin, Alhaji Lawan Liman ne ya bayyana hakan a wata taron manema labarai da ya kira jiya Laraba a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Liman, wanda shine kwamishinan lafiya na jihar ya ce, ana sa ran shugaban kasar da tawagar sa za su kaddamar da ayyuka guda 109 wanda suka hada da asibitoci, tituna, makarantu da sauransu.

Ku kalli ayyuka har 109 da shugaba Buhari zai dasa a jihar Zamfara

Ku kalli ayyuka har 109 da shugaba Buhari zai dasa a jihar Zamfara

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai kafa kotu na musamman don kwato kudin talakawa daga barayin gwamnati

Duk da cewa ba'a sanar da ranar da shugaba Buhari zai kai ziyarar ba, ana sa ran fadar shugaban kasar zata sanar da rannan ziyarar nan ba da dadewa ba.

"Mataimakin shugaban kasan zai fara ne da kaddamar da titin Dauran - Birnin Magaji - Kauran Namoda mai tsawon kilomita 61 sannan ya kadama da ayyukan ruwa kananan hukumomin Bakura da Zurmi.

"Akwai wasu ayyukan ruwa, tituna, da samar da wutan lantarki da gwamnatin jihar na Zamfara ta kaddamar a sabuwar Briged da ke Gusau," inji shi.

Ya kuma kara da cewa wasu mukarraban gwamnati da za su hallarci bikin sun hada da Ministan ayyuka, makamashi da gidaje, Babatunde Fashola, gwamnonin jihohin Sakkwato, Ebonyi, Adamawa, Katsina da Kano.

Saura sun hada Sarkin Musulmi, tsaffin gwamnonin jihohi, 'Yan majalisar tarayya, shugabanin al'umma da sauran mutane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel