Abinda nake bukata a wurin ‘yan jaridar Najeriya – Shugaba Buhari

Abinda nake bukata a wurin ‘yan jaridar Najeriya – Shugaba Buhari

A yau laraba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi ‘yan jarida da masu yada labarai das u ke yi masa adalci wajen watsa abinda ya fada ga jama’a.

Buhari ya bayyana cewar kamata ya yi ‘yan jaridar Najeriya su yi amfani da dama da kuma ‘yancin da gwamnati ta basu wajen wallafa zahirin duk abinda ya fada ba tare da kari ko ragi ba.

Kazalika ya yi kira ga ‘yan jarida das u kasance masu adalci, gaskiya da nuna kishin kasa yayin gudanar da aikin su.

Abinda nake bukata a wurin ‘yan jaridar Najeriya – Shugaba Buhari

Shugaba Buhari

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a wani sako na musamman ga ‘yan jarida da babban mai taimaka masa a bangaren yada labarai, Femi Adesina, a shiye-shiryen kokarin tunawa da ranar ‘yancin ‘yan jarida na duniya da za a yi gobe, Alhamis, 03 ga watan Mayu, 2018.

DUBA WANNAN: Kashi 70% na kodin din dake Najeriya a dajin Sambisa ake shanye shi - Sanatan Najeriya

Shugaban kasar ya kara kira ga ‘yan jarida das u kara yin taka-tsan-tsan yayin gudanar da aiyukan su musamman a wannan lokaci da babban zabe ke kara karatowa.

A yayin da muke kara tunkarar shekarar zabe, ina kira ga ‘yan jaridar mu das u mayar da hankali wajen watsa sahihan labarai ba tare da kokarin tauye gaskiya domin yin hakan shine babban ‘yancin dake cikin aikin jarida,’ a sakon shugaba Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel