Hukumar 'Yan sanda ta cafke mutane 10 da laifin kai farmaki Gidan Hadimin Gwamna Bagudu

Hukumar 'Yan sanda ta cafke mutane 10 da laifin kai farmaki Gidan Hadimin Gwamna Bagudu

Hukumar 'Yan sanda ta jihar Kebbi ta bayyana cewa tuni ta samu nasarar cafke wasu mutane da ake zargin su da laifin kai farmaki gidan Alhaji Faruk Enabo, babban hadimi na musamman ga gwamnan jihar, Alhaji Atiku Bagudu.

Kakakin hukumar DSP Mustapha Suleiman, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Birnin Kebbi a ranar yau ta Laraba.

Mustapha ya bayyana cewa, akwai yiwuwar abokan adawa ne na wasu mambobin jam'iyyu ke da alhakin wannan aika-aika a jihar.

Gwamnan jihar Kebbi; Atiku Bagudu

Gwamnan jihar Kebbi; Atiku Bagudu

A cewar sa, akwai adawa mai karfin gaske gamin da takun saka tsakanin kungiyoyi biyu daban-daban masu goyan bayan Buhari da Bagudu mabambanta ra'ayi.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya bayyana dalilin da yasa bai gamsu da batun 'Yan Sandan Jiha ba

Yake cewa, ana zargin daya daga cikin wannan kungiyoyi ne suka kai hari gidan Enabo sakamakon dangartakar dake tsakanin sa da daya daga cikin kungiyoyin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, an kai hari da muggan makamai gidan hadimin gwamna Bagudu a ranar Talatar da gabata, inda aka lallasa wani mai gadin gidan tare da raunata shi baya ga motoci da suka barnata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel