Da dumi-dumi: An cafke wani da ya kware wurin damfarar mutane a matsayin Magu na EFCC

Da dumi-dumi: An cafke wani da ya kware wurin damfarar mutane a matsayin Magu na EFCC

- Jami'an hukumar EFCC sun yi ram da wani sojin gona suna Felix Idowu, da ya kware wajen damfarar mutane a matsayin Ibrahim Magu mukaddashin shugaban EFCC.

- Kafin kama wannan sojan gona dai tsahon dalibin sashin koyar da kimiyyar siyasa ne na jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria kuma yana sayar da gidaje ne.

- Idewu ya sha karbe kudaden mutane da sunan shi Ibrahim Magu ne na EFCC, kuma an same shi da wasu takardu da aka kwaikwayi san hannun shugaban EFCC Ibrahim Magu.

A cikin wani jawabi da hukumar ta bayyanawa majiyarmu, EFCC ta ce, kafin kama wanda ake zargin, sun samu bayanan sirri dake nuna cew, wasu na amfani da sunan hukumar wajen tambayar mutane kudi domin su kashe duk wata matsala idan ta hada wanda suke son karbar kudi da EFCC.

Da dumi-dumi: An cafke wani da ya kware wurin damfarar mutane a matsayin Magu na EFCC

Jami'an hukumar EFCC

A irin wannan yanayi ne kuma suka samu ya fado komarsu ta hanyar hada shi da wani jami'insu na boye a matsayin mataimaki ga wanda suke son karbar kudi a wurinsa, a yayin waccan tattaunawa ne kuma jami'in na EFCC ya ja shi har zuwa wata babban kntin saida kayayyaki dake Wuse, inda acan ne aka samu nasarar damke shi a ranar Litinin 30 ga watan da ya gabata.

DUBA WANNAN: Kashi 70% na kodin din dake Najeriya a dajin Sambisa ake shanye shi - Sanatan Najeriya

yayin binciken mutar da yazo da ita ne Lexus EX 350 aka samu takardu da yawa ciki harda wacce aka gudanar da binciken karya da sunan EFCC mai lamba ‘Ref No: CTGI/6/vol.1 da tambarin hukumar da kuma takarda dauke da satar sa hannun shugaban hukumar Ibrahim Magu.

Nan ba da jimawa ba ne da zarar an kammala bincike hukumar zata mika shi gaban kuliya domin girbar abinda ya shuka. inji kakakin hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel