Yajin Aikin Ma'aikatan Lafiya: Wani Dattijo 'Dan Shekara 50 ya Kashe Kansa a jihar Oyo

Yajin Aikin Ma'aikatan Lafiya: Wani Dattijo 'Dan Shekara 50 ya Kashe Kansa a jihar Oyo

Hukumar kula da asibitin University College Hospital, UCH dake garin Ibadan ta bayyana a ranar Laraba ta yau cewa, wani dattijo da har yanzu ba a gano sunan sa ba da gangan ya dirgo daga saman gini mai tsawon hawa shidda na asibitin.

Kakakin asibitin Deji Bobade, shine ya tabbatar da afkuwar wannan lamari yayin ganawa da manema labarai a babban birnin na Ibadan dake jihar Oyo.

Deji ya bayyana cewa, wannan Dattijo dai bincike ya tabbatar da cewa ya hau saman ginin asibitin da gangan inda ya dirgo da nufin salwantar da rayuwar sa kuma cikin ikon Rabbani ya cimma manufar sa.

Gawar Dattijon yayin da ake killace ta

Gawar Dattijon yayin da ake killace ta

A yayin da ma'aikatan Lafiya karkashin kungiyar JOHESU ke ci gaba da gudanar da yajin aiki a fadin kasar nan, ba bu ko wani ma'aikacin lafiya da aka yarda ya fita bakin aiki, inda wannan dattijo ya cika ba tare da an kai dauki a gare shi ba.

Da misalin karfe 9.00 na safiyar yau din mutane dake gudanar da harkokin gaban su suka ji sauti na fadowar abu mai nauyi, inda bayan sun bincika sai suka yi kacibus da gawar wannan Dattijo da ake zargin shekarun sa a duniya na tsakanin 50 zuwa 60.

KARANTA KUMA: Hukumar Alhazai Reshen Jihar Kano ta bayyana adadin Kudin Kujerun bana

A yayin tuntubar Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Adekunle Ajisebutu ya tabbatar da wannan lamari inda ya umarci jami'an na 'yan sanda akan killace gawar dattijon a ma'ajiyar gawa ta asibitin.

Bincike dai ya tabbatar da cewa ba bu wata alama ta fayyace wannan dattijo in ban da takalmin soso dake sanye a sawayen sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel