Yan Shi’a sun sake yin zanga-zanga a birnin tarayya, suna bukatar a saki El-Zakzaky

Yan Shi’a sun sake yin zanga-zanga a birnin tarayya, suna bukatar a saki El-Zakzaky

- Kungiyar ‘yan Shi’a a ranar Laraba sukayi zanga-zanga a birnin tarayya, inda suka bukaci a saki shugabansu Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky wanda yake tsare a birnin tarayyar tun shekarar 2015

- Daruruwan ‘yan kungiyar wadanda suka hada da mata da yara sun rike takardu da aka rubuta maganganu na bukatar a saki Sheikh Zakzaky

- ‘Yan kungiyar sun jera layi wurin gudanar da zanga-zangar cikin lumana, don gudun kawo cushewar hanya tare da jami’an ‘Yan Sanda biye dasu don kada su karya doka

Kungiyar ‘yan Shi’a a ranar Laraba sukayi zanga-zanga a birnin tarayya, inda suka bukaci a saki shugabansu Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky wanda yake tsare a birnin tarayyar tun shekarar 2015.

Daruruwan ‘yan kungiyar wadanda suka hada da mata da yara sun rike takardu da aka rubuta maganganu na kamar haka: “Buhari must release Sheikh Ibrahim Zakzaky”, Sheikh Ibrahim Zakzaky must be released”, da makamantan haka.

‘Yan kungiyar sun jera layi wurin gudanar da zanga-zangar cikin lumana, don gudun kawo cushewar hanya tare da jami’an ‘Yan Sanda biye dasu don kada su karya doka.

Shugaban matasan kungiyar wadanda ake kira da Hurras, Yaqub Idris, yace an tsara zanga-zangar don bukatar a saki shugabansu.

Yan Shi’a sun sake yin zanga-zanga a birnin tarayya, suna bukatar a saki El-Zakzaky

Yan Shi’a sun sake yin zanga-zanga a birnin tarayya, suna bukatar a saki El-Zakzaky

Kungiyar sun bayyana abubuwa da dama da suke zargin cewa gwamnatin APC ce ta shiryasu don rashin kaunar kungiyar, inda suka bayar da misalin abunda ya wakana tsakanin jami’an tsaro da ‘yan kungiyar a ofishin kare hakkin dan adam dake birnin tarayya cikin kwanakinnan.

KU KARANTA KUMA: Furucin Trump kan Najeriya na haifar da cece-kuce

Kungiyar suna kira ga Buhari da ya bi ka’idar dokar kasa ya gaggauta sakin shugabansu, da matarsa Malama Zeenatu da kuma wadanda aka kama lokacin rikicin Zaria.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel