Buratai ya gargadi sojoji akan nuna wasu halaye a dandalin sada zumunta

Buratai ya gargadi sojoji akan nuna wasu halaye a dandalin sada zumunta

Shugaban hafsin sojojin Najeriya, Laftanant Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi gargadi ga hafsoshin hukumar su dena amfani da kafafen sada zumunta wajen tattauna tsarin ayyukun hukumar ko kuma yin korafi saboda hakan na kawo nakasu ga tsaron kasa.

Buratai, wanda ya samu wakilcin shugaban tsare-tsare na hukumar, Manjo Janar Rasheed Yusuf ya yi gargadi cewa laifi ne tattauna harkokin hukumar a kafafen sada zumunta inda ya kara da cewa hukumar ta samar da hanyoyin gabatar da korafe-korafe.

Hukumar soji tayi wani gargadi na musamman game da amfani da kafafen sada zumunta

Hukumar soji tayi wani gargadi na musamman game da amfani da kafafen sada zumunta

Shugaban sojin ya yi wannan gargadin ne yayin da yake jawabi a wata taron kara wa juna ilimi da aka shirya wa ma'aikatan sashin ajiye bayyanan tsaro na hukumar a Command Officers Mess da ke Abuja.

KU KARANTA: Gaskiya ta fara bayyana: An leko sakamakon kwamitin binciken badakalar zabe a Kano

Buratai ya kara da cewa hukumar sojin ta kafa wani sashi na musamman da zai rika sa ido kan abubuwan da hafsoshin rundunar ke tattaunawa a kafafen sada zumunta na zamani.

Ya ce, "Fitowan kafafen sada zumunta ya zo da wani kallubalen tsaro wanda wasu gurbatatu cikin ma'aikatan mu ke yin amfani da kafafen ta hanyoyin da bai dace ba.

"Hukumar sojin Najeriya tana da dokoki da suka hana hafsoshin soji tattauna batuttuwan da suka shafi ayyuka da kuma sirri na kasa.

"Abin takaici ne a samu wasu daga cikin hafsoshin sojin suna gabatar da korafe-korafen su da fadin bayyanan sirri da kafafen sada zumunta alhalin hukumar ta samar da hanyoyin shigar da irin wannan korafe-korafen".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel