Duniya juyi-juyi: Wata Mata ta nemi kotu ta raba aurenta da Mijinta don rashin kulawa

Duniya juyi-juyi: Wata Mata ta nemi kotu ta raba aurenta da Mijinta don rashin kulawa

- Rashin kulawar da wani miji ke bawa matarsa na barazanar kawo ƙarshen aurensu

- Matar magidancin ta maka shi kotu don neman alƙali ya tursasa ya sauwaƙe mata

A yau Laraba ne wata matar aure mai suna Nazira Ahmad ta kai ƙara gaban kotun shari'ar musulunci dake Magajin Gari na jihar Kaduna, domin roƙon a raba aurensu da mijinta Sirajo Adullahi a dalilin rashin kulawa da yake mata.A yau Laraba ne wata matar aure mai suna Nazira Ahmad ta kai ƙara gaban kotun shari'ar musulunci dake Magajin Gari na jihar Kaduna, domin roƙon a raba aurensu da mijinta Sirajo Adullahi a dalilin rashin kulawa da yake mata.

Duniya juyi-juyi: Wata Mata ta nemi kotu ta raba aurenta da Mijinta don rashin kulawa

Duniya juyi-juyi: Wata Mata ta nemi kotu ta raba aurenta da Mijinta don rashin kulawa

Mai ƙarar ta kuma shaidawa kotun cewa, mijin nata na kuma zarginta da sanyawa abincinsa shekafar ɓera, ga na jaki da yake lakaɗa mata kusan koyaushe.

KU KARANTA: Tsaro: Yan sanda sun damke yan kungiyar asiri da yan fashi da makami 25 da bindigu masu yawa

Nazira dai tace mijin nata baya bata kulawa har ta tsawon sati uku yayin da ta tafi gidan iyayenta, ta roƙi kotun da ta raba aurensu.

Sannan kuma ta ce, Minjin nata Abdullahi ya daina ciyar da ita da ɗanta kuma baya kula da lafiyarsu domin bata muhimmancin a gare shi.

Shi kuma Sirajo da ake ƙarar, ya musanta dukkan nin laifin da aka faɗa tare da cewa ya samar da abinci a koyaushe ga iyalin nasa gami da kula da lafiyarta kuma baya dukanta kamar yadda ta faɗa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel