So na yi ayi banza da Obasanjo bayan da ya soki Gwamnati na a wasika - Inji Buhari

So na yi ayi banza da Obasanjo bayan da ya soki Gwamnati na a wasika - Inji Buhari

- Shugaba Buhari ya tabo maganar wasikar Obasanjo ta kwanaki

- Shugaban kasar yace bai yi niyyar maidawa Obasanjo martani ba

- A wasikar dai Obasanjo ya soki Gwamnatin Shugaban kasa Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi magana game da doguwar wasikar da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya rubuta a kan Gwamnatin sa kwanakin baya a makon nan.

So na yi ayi banza da Obasanjo bayan da ya soki Gwamnati na a wasika - Inji Buhari

Buhari yace ko kadan bai so ya maidawa Obasanjo martani ba

Shugaba Buhari ya bayyana wannan ne lokacin da yayi hira da Gidan Rediyon VOA na Amurka a Babban Birnin Washington. Shugaban kasar yake cewa zagin sa kurum tsohon Shugaba Obasanjo yayi a budaddiyar wasikar da ya saki kwanaki.

KU KARANTA: Buhari yayi magana game da kashe-kashen Najeriya

A hirar da yayi a Ranar Talata, Shugaban kasar ya bayyana cewa bai yi niyyar maidawa Olusegun Obasanjo martani ba sai dai Ministan yada labaran kasar watau Lai Mohammed ne ya nemi a bayyawa Obasanjo irin kokarin Gwamnatin sa.

Idan ba ku manta ba bayan Olusegun Obasanjo ya aiko wasikar ta sa wanda har yayi kira ga Shugaba Buhari ya hakura da mulkin Najeriya bayan 2019, Gwamnatin Tarayya ta maida masa martani inda ta jero masa irin nasarorin Gwamnatin nan.

Dama kun ji cewa Raymond Dokpesi ya Gwamnatin Buhari babban Kotun Tarayya a karshen watan jiya inda yake neman a biya shi makudan kudi na bata masa suna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel