Furucin Trump kan Najeriya na haifar da cece-kuce

Furucin Trump kan Najeriya na haifar da cece-kuce

Kalamin da Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya furta na cewa ba za su lyarda da kisan da ake yiwa kiristoci a Najeriya ba ya jawo cece-kuce daga mabiya manyan addinan kasar biyu.

Kungiyar Kiristocin Najeriya wato CAN tace tayi amanna da kalamin da Trump yayi a lokacin ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai White House.

Sai dai wata kungiyar kare hakkin Musulmi a Najeriya wato MURIC ta yi Allah wadai da kalaman inda ta ce wani kokari ne na ba wa kiristoci kwarin gwiwar yakar musulmi a kasar.

Furucin Trump kan Najeriya na haifar da cece-kuce

Furucin Trump kan Najeriya na haifar da cece-kuce

Idan dai bazaku manta ba Trump ya ce yana sha'awar zuwa Najeriya inda ya siffanta kasar a matsayin wata kasa mai ban mamaki.

KU KARANTA KUMA: Rikicin Makiyaya: Mutanen da aka kashe a Zamfara sunfi wadanda aka kashe a Benue da Taraba baki daya - Buhari

Shugaban Amurka ya bayyana Najeriyar a matsayin kasar da cin-hanci da rashawa suka yi wa katutu amma ya ce gwamnatin Shugaba Buhari ta rage matsalar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel