IGP Idris ya bayyana gaban majalisar dattawan Najeriya kan al'amarin Dino Melaye

IGP Idris ya bayyana gaban majalisar dattawan Najeriya kan al'amarin Dino Melaye

Wakilin Sifeto Janar na yan sanda, IGP Ibrahim Kpotum Idris, ya bayyana gaban majalisar dattawan Najeriya a yau Laraba, 2 ga watan Mayu, 2018.

Babban hafsan hukumar yan sandan ya turo wakili ne yau bayan ya fifita raka shugaba Buhari jihar Bauchi a makon da ya gabata akan gayyatar da majalisan dattawa ta masa.

A yanzu haka, wakilin da ya turo na cikin majalisan inda yake amsa tambayoyi daga bakin yan majalisan akan al'amuran da suka shafi damke Sanata Dino Melaye.

Wanna abu bai yiwa sanatocin majalisan dattawa dadi ba inda suka nuna bacin ransu tun makon da ya gabata.

IGP Idris ya bayyana gaban majalisar dattawan Najeriya kan al'amarin Dino Melaye

IGP Idris ya bayyana gaban majalisar dattawan Najeriya kan al'amarin Dino Melaye

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa wasu mutane masu fuska rufe sun dira majalisar dokokin tarayya dauke da manyan makamai wanda ya baiwa mutane tsoro.

Majiyarmu ya bayyana cewa an ga wani gardin kato a gaban majalisar dattawa inda aka dauke sandar majalisa mako biyu da suka gabata dauke da bindiga AK47 da safen nan.

KU KARANTA: Buhari yace an kashe mutane ya fi a kirga a Zamfara

Kana an ga ire-irensu a wajaje daban –daban a cikin majalisan. Ana sa ran cewa hakan na faruwa ne saboda sifeto janar nay an sandan zai bayyana gaban yan majalisan dattawa a yau bisa ga al’amarin damke sanata Dino Melaye da kuma wasu abubuwa da suka shafi tsaron kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel