Rashawa: Buhari yace za’a kirkira kotuna na musamman, ya gargadi barayin gwamnati

Rashawa: Buhari yace za’a kirkira kotuna na musamman, ya gargadi barayin gwamnati

- Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa zata kirkira sababbin kotuna na musamman ta masu rashawa

- Shugaba Buhari yace kotun za’a bata damar karbe kudade da kadarorin ‘yan Najeriya wadanda suka gaza bayyana yanda akayi suka samu irin wannan dukiya

- Shugaban kasar yace shi da kansa zai zabo Alkalan kotunan, kuma zai basu lokaci da duk wata shaida kamar ta bayanin banki da kadarori wadanda mutane suka mallaka da kuma abunda suke samu a wurin aiki

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa zata kirkira sababbin kotuna na musamman ta masu rashawa.

Shugaba Buhari yace kotun za’a bata damar karbe kudade da kadarorin ‘yan Najeriya wadanda suka gaza bayyana yanda akayi suka samu irin wannan dukiyar.

“Za’a tambayesu inda suka samu banbanci na tsakanin dukiyarsu da kuma abunda ake biyansu a wurin aiki, ko kuma a karbe komai kuma a hukuntasu,” Buhari ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai na Amruka a ziyarar da ya kai a kasar.

Rashawa: Buhari yace za’a kirkira kotuna na musamman, ya gargadi barayin gwamnati
Rashawa: Buhari yace za’a kirkira kotuna na musamman, ya gargadi barayin gwamnati

Shugaban kasar yace shi da kansa zai zabo Alkalan kotunan, kuma zai basu lokaci da duk wata shaida kamar ta bayanin banki da kadarori wadanda mutane suka mallaka da kuma abunda suke samu a wurin aiki.

Gashi saura watanni 10 a sake sabon zabe saboda haka kotunan Buhari na musamman bazasu fara aiki ba sai idan ya koma kan kujerarsa ta shugaban kasa a karo na biyu.

KU KARANTA KUMA: An kama wani mutum bayan yayi barazanar sace tsohon ubangidansa saboda ya koreshi daga aiki

A baya Legit.ng ta rwaito cewa, Shugaba Muhammadu Buhari ya aikowa matasan Najeriya da sako, inda ya bukacesu dasu koma harkar noma saboda nan ne inda kasar ta dosa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng