Nigerian news All categories All tags
Malaman addinan Arewa sun soma azumin kwana 30 don samun sabon shugaban kasa a 2019

Malaman addinan Arewa sun soma azumin kwana 30 don samun sabon shugaban kasa a 2019

Wasu malaman addinai da suka hada da na musulmai da kuma kiristoci sun umurci mabiyan su da su da fara azumin kwanaki 30 domin rokon Allah ya sa ayi zaben shekarar 2019 lafiya ya kuma ba kasar nan sabon shugaba a zaben na game gari.

Shugaban hadakar malaman ne dai kuma Ciyaman na kungiyar shugabannin kiristoci mai suna Fasto Aminchi Habu ya bayyanawa manema labarai hakan a garin Abuja.

Malaman addinan Arewa sun soma azumin kwana 30 don samun sabon shugaban kasa a 2019

Malaman addinan Arewa sun soma azumin kwana 30 don samun sabon shugaban kasa a 2019

KU KARANTA: Mahara sanye da kayan sojoji sun yi ta'asa a Kaduna

A cewar sa, azumin sun fara shi ne tun 16 ga wannan watan kuma za su kammala shi a ranar 16 ga wata mai kama inda kuma a karshe za suyi babban taron addu'a domin samarwa kasar nan mafita a zaben mai zuwa.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a wata tattaunawa da yayi da gidan yada labarai na Muryar Amurka ya dora alhakin tabarbarewar harkoki a kasar Najeriya kacokam a kan tsaffin shugabannin kasar.

Haka zalika shigaban ya kuma kara yin haske game da kalaman sa akan matasa da suka yi ta jawo cece-kuce kimanin makwonni biyu da suka shude inda yace 'yan jarida ne suka jirkita maganar ta sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel