Nigerian news All categories All tags
Abun takaici ne Buhari baya yabon kowa sai kan sa - Hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo

Abun takaici ne Buhari baya yabon kowa sai kan sa - Hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo

Hadakar nan ta wasu zaratan 'yan Najeriya da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya assasa da zummar maido da martabar kasar a bisa turba daidaitacciya watau Coalition for Nigeria Movement (CNM) ta yi wa shugaba Buhari wankin babban bargo.

Hadakar ta Coalition for Nigeria Movement dai kamar yadda muka samu ta na maida martani ne ga shugaban kasar game da kalaman sa a yayin wata fira da yayi lokacin ziyarar sa kasar Amurka game da yadda tsaffin shugabannin kasar Najeriya suka lalata kasar.

Abun takaici ne Buhari baya yabon kowa sai kan sa - Hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo

Abun takaici ne Buhari baya yabon kowa sai kan sa - Hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo

KU KARANTA: Dalilin da ya sa Oyegun ba zai yi takarar shugabancin APC ba

Legit.ng ta samu cewa hadakar ta CNM ta bayyana takaicin ta ne a kan yadda shugaban a duk inda ya bode baki baya yabon kowa sai kan sa.

A wani labarin kuma, Fadar shugaban kasar Najeriya a ranar Talatar da ta gabata da yayi daidai da ranar ma'aikata a dukkan fadin Najeriya ta fallasa wani abu da ta kira kullalliyar da gwamnatin shugaba Jonathan ta shirya yi na korar ma'aikata da dama.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata makala da maitaimakawa shugaban kasar na musamman kar harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar inda ya ce tuni har shire-shiren dabbaka hakan yayi nisa kafin Allah ya kawo gwamnatin Buhari.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel