Buhari ga Matasa: Ku rungumi sana’ar Noma domin ku tsira da mutuncinku

Buhari ga Matasa: Ku rungumi sana’ar Noma domin ku tsira da mutuncinku

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci matasan Najeriya, musamman na Arewacin kasar dasu rungumi sana’ar noma domin su tsira da mutuncinsu, musamman duba da yadda fannin noma ke samun cigaba a Najeriya.

Buhari ya bayyana haka ne a yayin wata ganawa da yayi da tawagar hamshakan yan kasuwan kasar Amurka kuma kwararru a harkar noma, da takwarorinsu yan Najeriya, daga ciki har da fitaccen attajiri Aliko Dangote.

KU KARANTA: Karin albashi: Bani gishiri in baka manda zamu yi da yan siyasa a zaben 2019 – Kungiyar kwadago

Daily Nigerian ta ruwaito Buhari na kokawa kan rashin aiki yi da matasan Najeriy ke fama da ita, inda yace ya zama wajibi a taimaki matasa wajen shirya musu gaba mai kyau, tare da shawartarsu da su rungumi Noma, domin nan gaba Noma zata zama muhimmiyar sana’a.

Hakazalika Buhari ya dau alwashin bada gudnmuwa ga matasan da suka nuna sha’awarsu wajen kirkire kirkire don samun matasa da zasu amfani al’umma a gaba, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

“Mun gano cewar da tun a baya mun baiwa noma fifiko da bamu tsinci kanmu cikin halin da muke ciki ba a yanzu, amma muna bashi muhimmanci da ya dace a yanzu, don haka matasan da suka yi karatu da wadanda basu yi ba su koma gona don su tsira da mutuncinsu.” Inji Buhari.

Daga karshe Buhari ya yi maraba da hannayen jari da kamfanonin Amurka zasu zuba a Najeriya da suka hada da kamfanin taki na Dangote da babu kamarsa a duk fadin Afirka, wanda zai fara aiki a watan Yuli, kamfanin sarrafa maganin kwari, kamfanin sarrafa tumatir na Heinz, kamfanin kera tarakta John Deer da zai samar da Tarakta dubu goma a shekaru hudu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel