Nigerian news All categories All tags
Karya ne batun cewa wuta ta kama a CBN

Karya ne batun cewa wuta ta kama a CBN

- Labarin da ake ta yada wa dake nuna cewa babban bankin Najeriya ya kama da wuta ba gaskiya bane

- Wasu masu wucewa ta wurin bankin sunga hayakin janaretone daga nesa a cikin ginin bankin inda sukayi zaton hayakin na gobara ne

Karya ne batun cewa wuta ta kama a CBN

Karya ne batun cewa wuta ta kama a CBN

Labarin da ake ta yada wa dake nuna cewa babban bankin Najeriya ya kama da wuta ba gaskiya bane.

Wasu masu wucewa ta wurin bankin sunga hayakin janaretone daga nesa a cikin ginin bankin inda sukayi zaton hayakin na gobara ne.

DUBA WANNAN: Wata kungiya ta bukaci da a tsige gwamna Ganduje

Babban bankin Najeriya dai yana da na'urori na tsaro wanda koda hayaki ne ya taso zai sanar da ma'aikatan wurin cewa akwai matsala ballantana kuma gobara, to abinda ya faru kenan, hayaki ne ya tashi a jikin wani inji sai na'urorin tsaron suka sanar da ma'aikatan bankin, cikin kankanin lokaci aka gyara komai aiki ya cigaba da gudana kamar yanda aka saba.

Tuni dai aka kashe janareton da yake fitar da hayakin inda kowa ya koma bakin aikin shi sannan injiniyoyi suka cigaba duba matsalar janareton.

Muna shaidawa al'ummar kasar nan cewa babu wata wuta data tashi a CBN.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel