Nigerian news All categories All tags
2019: A jiha daya katchal, magoya bayan Buhari sun siya masa motocci 124 na kamfen

2019: A jiha daya katchal, magoya bayan Buhari sun siya masa motocci 124 na kamfen

- Wasu jiga-jigai na jam'iyyar APC a jihar Kebbi sun sayi motocci guda 124 saboda yakin neman zaben Buhari da Bagudu

- Cikin wadanda suka bayar da gudunmawar har da Sanata Aliero, Bello Bagudu da kwamishinonin jihar ta Kebbi

- Sanata Aliero ya shawarci magoya bayan jam'iyyar su mallaki katin kada kuri'a don su zabi APC

Wasu masu hannu da shuni a jami'iyyar APC reshen jihar Kebbi sun bayar da siya wa shugaba Muhammadu Buhari motocin guda 124 don gudanar da yankin neman zaben 2019.

An gabatar da motoccin ne a taron kaddamar ta kwamitin zartarwa na kungiyar yakin neman zaben Buhari da Bagudu a zaben 2019 a jihar Kebbi.

2019: A jiha daya katchal, magoya bayan Buhari sun siya masa motocci 124 na kamfen

2019: A jiha daya katchal, magoya bayan Buhari sun siya masa motocci 124 na kamfen

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya aike da muhimmin sako ga matasan Najeriya

Wadanda suka bayar da gudunmawan motoccin sun hada da Sanata Adamu Aliero wanda ya bayar da motocci 6, Sakataren gwamnatin tarayya na jihar Kebbi ya bayar da motocci biyar, Bello Bagudu ya bayar da motocci 12.

2019: A jiha daya katchal, magoya bayan Buhari sun siya masa motocci 124 na kamfen

2019: A jiha daya katchal, magoya bayan Buhari sun siya masa motocci 124 na kamfen

Kazalika, Kowanne kwamishina a jihar ta Kebbi ya bayar da gudunmawar mota guda daya.

A jawabin da yayi wajen taron, Sanata Aliero ya yi kira ga magoya bayan jam'iyyar su tabbata sun karbi katin kada kuri'arsu saboda su zabi jam'iyyar ta APC idan zaben ya zo.

Tsohon gwamnan kuma ya shawarci 'ya'yan jam'iyyar su rungumi sulhun da akeyi a jam'iyyar kafin gudanar da babban taron jam'iyyar da za'a gudanar a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel