Gaskiya ta fara bayyana: An leko sakamakon kwamitin binciken badakalar zabe a Kano

Gaskiya ta fara bayyana: An leko sakamakon kwamitin binciken badakalar zabe a Kano

- INEC ta kafa kwamiti don bincike akan yiwa wadanda shekarun su baikai ba rijista

- Wata majiya daga hukumar INEC din ne ta wallafa wasu sassan cikin rahoton kwamitin

- Binciken ya nuna cewa hukumar INEC bata da laifi a saboda ba'ayi amfani da rajisatanta ba wajen tantance masu kada kuri'an

Wasu bayanai daga cikin rahoton kwamitin bincike da aka kafa don gano kwa-kwaf kan zargin da ake yi na cewa kananan yara da basu isa jefa kuri'a ba sun dangwala zaben a jihar Kano ya fito fili.

Rahoton ya bayyana cewa hukumar zabe ta Kano (KANSIEC) bata yi amfani da katin zabe wanda INEC ta tanadar don tantance da masu zaben kananan hukumomi da aka gudanar a watan Fabrairu.

Gaskiya ta fara bayyana: An leko sakamakon kwamitin binciken badakalar zabe a Kano

Gaskiya ta fara bayyana: An leko sakamakon kwamitin binciken badakalar zabe a Kano

Kamar yadda wata kwakwarar majiya tace, Hukumar ta INEC ta gano cewa akwai wasu tsirarun yara da akayi wa rajistan zabe a 2011 da 2015 amma babu wasu hujjoji da ke nuna cewa kananan yara sun kada kuri'a a zaben kananan hukumomi da akayi a jihar.

KU KARANTA: Asirin wata mata dake koyawa kwailaye karuwanci ya tonu

Duk da cewa hukumar zabe na jihar Kano ce ta gudanar da zaben kananan hukumomin, masu sharhi a kan harkokin siyasa da dama sun danganta zaben da hukumar INEC inda suka ce ita zata dauki matakin gyra kan rajistan da akayi wa kananan yara.

Dangane da hotunan da aka dinga yadawa a kafofin yada labarai ana gama zaben binciken da aka gudanar ya nuna cewa wadannan hotunan ajjiyayyu ne da aka samo a yanar gizo wanda akayi dauka tun kafin zaben da aka gudanar 10 ga watan Febrairu.

"A takaice dai wadannan hotuna tsofaffi ne wadanda suke yawo a kafafin sadarwa tun 2017, mafi yawan bidiyon an samesu daga kananan hukumomi inda wadanda ba'a sani ba suka kada kuri'a ba tare da katin zabe ba" inji rahoton.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel