Shugaba Buhari ya aike da muhimmin sako ga matasan Najeriya

Shugaba Buhari ya aike da muhimmin sako ga matasan Najeriya

- Shugaba Muhammadu Buhari ya shawarci matasan Najeriya sun tsundunma cikin ayyukan noma

- Shugaban kasan ya ce akwai garabasa sosai da fannin aikin noman

- Buhari ya ce kamfanonin noma guda 6 daga Amurka zasu bude rassan su a Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya aike da muhimmin sako ga matasan Najeriya inda ya shawarce su da su tsunduma cikin fannin ayyukan noma saboda nan kasar ta mayar da hankali.

Shugaba Buhari ya furta wannan magana ne yayin da yake ganawa da wasu kamfanonin noma na kasar Amurka guda shida a ranar Litinin 30 ga watan Afrilu.

Shugaba Buhari ya aike da muhimmin sako ga matasan Najeriya

Shugaba Buhari ya aike da muhimmin sako ga matasan Najeriya

A wata sanarwa da ta fito daga hannun mataimakin shugaban kasa na musamman a fanin kafafen yadda labarai Garba Shehu ranar 1 ga watan Mayu, shugaban kasan ya ce matasa za su samu ayyukan yi sosai a fanin aikin noman.

KU KARANTA: An bawa hammata iska tsakanin ma'aikata da 'yan kungiyar kwadago a filato

Shugaban kasa ya ce tattaunawan da ya yi da kamfanonin noma na kasar Amurka zai haifar ga alheri ga matasan Najeriya inda yace kamfanonin zasu bude rassan su a Najeriya.

A cewar shugaban kasan, " Duk da cewa mun makara, mun gano cewa abinda ya kamata muyi shine saka hannu jari a fanin noma. Muna kokarin mu tabbatar da cewa mun magance matsalar karancin abinci a kasar mu. Muna kira da matasan Najeriya wadanda sukayi karatu da wanda basuyi ba duk su rungumi aikin noma saboda su mutunta kansu.

"Aikin noma na samar wa miliyoyin matasa ayyukan kuma muna kokarin ganin mun samar da ayyukan yi da wadata kasa da abinci ne. Mai yiwuwa kafafen yadda labarai basu san irin ayyukan da muke yi ba amma zamu basu mamaki da nasarorin da zamu samu."

Shugaban kasan yana maraba da masu saka hannun jari daga yan kasuwa daga Najeriya da takwarorinsu na kasar Amurka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel