Nigerian news All categories All tags
Asalin ranar ma'aikata da dalilin tunawa da ita duk shekara

Asalin ranar ma'aikata da dalilin tunawa da ita duk shekara

A yau, Talata, 1 ga watan Mayu ma'aikatan Najeriya ke shiga sahun ma'aikatan duniya domin murnar zagayowar ranar ma'aikata ta duniya.

Ma'aikata, kusan ko ina a fadin duniya, na fuskantar kalubale ta fuskar yanayin aiki da albashi da alawus.

A karni na 18 ne (1860) ma'aikata suka fara fafutikar neman a rage yawan sa'o'in aiki daga 16 ko 10 zuwa 8 a kowacce rana.

A ranar 1 ga watan Mayu, 1886, ma'aikata a kasar Kanada da Amurka sun gudanar da zanga-zangar lumana domin neman a mayar da sa'o'in aiki su koma takwas.

Kwana biyu da fara zanga-zangar (3 ga watan Mayu, 1886) sai aka samu hargitsin da ya kai ga jami'an 'yan sanda sun kashe wasu daga cikin masu zanga-zangar.

Bayan kisan ma'aikatan ne sai wata sabuwar zanga-zangar ta barke har ta kai ga wulla bam a sansanin zanga-zangar a yayin da 'yan sanda ke kokarin tarwatsa taron masu zanga-zangar.

Asalin ranar ma'aikata da dalilin tunawa da ita duk shekara

Bikin ranar ma'aikata na yau

'Yan sanda bakwai sun mutu, yayin da jama'a da dama suka samu raunuka.

Duk da ba ma'aikatan e suka wulla bam din ba, an kama shugabannin kungiyar ma'aikata su takwas tare da gurfanar da su gaban kotu bisa tuhumar kashe jami'an tsaro.

An yankewa hudu daga cikin su hukuncin kisa, daya ya mutu a yayin da suke tsare, an yankewa uku hukuncin daurin rai-da-rai kafin daga bisani a yafe masu.

DUBA WANNAN: Dan sandan Najeriya da bai taba karbar cin hanci ba ya samu kyauta daga BBC

A kokarin tunawa da wadannan 'yan gwagwarmayar ne, kungiyar ma'aikata ta duniya ta kirkiro hutun sa'o'i takwas, duk ranar 1 ga watan Mayu, ga ma'aikatan duk duniya a shekarar 1889.

An fara hutun ranar ma'aikata a Najeriya a 1980 a jihar Kano karkashin shugabancin jam'iyyar PRP kafin daga bisani gwamnatin tarayya ta mayar da ita ranar hutu a kasa baki daya a shekarar 1981.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel