Nigerian news All categories All tags
'Yan bindiga sun kashe wani hadimin gwamnan Najeriya

'Yan bindiga sun kashe wani hadimin gwamnan Najeriya

A daren jiya Litinin misalin karfe 10 na dare ne wasu 'yan bindige sun kashe wani hadimin gwamna Seriake Dickson na jihar Bayelsa.

Yan bindigan sun harbe Ebikimi Okoringa ne a kauyen su da ke karamar hukumar Kolokuma-Opokuma da ke jihar.

Marigayin ya rike mukamin Kansila sau biyu kuma ya taba zama Ciyaman na rikon kwarya a karamar hukumar su.

'Yan bindiga sun kashe wani hadimin gwamnan Najeriya

'Yan bindiga sun kashe wani hadimin gwamnan Najeriya

KU KARANTA: Gwamnati ta haramta sarrafa maganin tari mai sinadarin kodin

Wani mazaunin kauyen da ya bukaci a sakaya sunansa yace yan bindigan sunyi kwantar bauna ne a gidan marigayin kuma suka bude masa wuta yayin da ya fito daga motarsa.

"Sun boye cikin duhu ne suka jira shi, sun bude masa wuta ne yayin da ya fito daga motarsa ya nufi kofar shiga gidansa.

"Harsashin farkon ya same shi a hannu ne sai ya fara gudu amma yan bindigan suka bishi har sai da ya kai ga faduwa kuma suka kara harbinsa a jiki," inji majiyar.

Majiyar yace 'yan bindigar sun tabbatar ya mutu kafin suka tafi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel