Nigerian news All categories All tags
Trump ya nemi goyon bayan Najeriya don basu bakuncin gasar cin kofin duniya na 2026

Trump ya nemi goyon bayan Najeriya don basu bakuncin gasar cin kofin duniya na 2026

- Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya nemi Najeriya da kuma sauran kasashen nahiyar Afirka dasu goyi bayan kasashen hadin guiwa da suka hada da Canada, Amurka da kuma kasar Mexico akan neman karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a shekarar 2026

Trump ya nemi goyon bayan Najeriya don basu bakuncin gasar cin kofin duniya na 2026

Trump ya nemi goyon bayan Najeriya don basu bakuncin gasar cin kofin duniya na 2026
Source: Depositphotos

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya nemi Najeriya da kuma sauran kasashen nahiyar Afirka dasu goyi bayan kasashen hadin guiwa da suka hada da Canada, Amurka da kuma kasar Mexico akan neman karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a shekarar 2026.

DUBA WANNAN: Jami'ar Musulunci ta dakatar da dalibai 23 bisa laifin Zina a cikin makaranta

Shugaba Trump yayi kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labaru a fadar sa ta White House, jim kadan bayan sun kammala tattaunawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wanda ya kai ziyarar kwana uku kasar ta Amurka.

Trump yace Amurka zata saka ido don ganin kasashen da zasu goyi bayan aniyarta ta karbar bakuncin gasar cin kofin duniyar.

A ranar 13 ga watan Yunin wannan shekarar ne hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA zasu jefa kuri'a domin tantance kasar da za'a baiwa damar karbar bakuncin gasar cin kofin na duniya tsakanin kasar Amurka da kuma kasar Morocco dake nahiyar Afirka.

Sai dai kuma da akwai yiwuwar kalaman da shugaba Trump yayi yasa kasar ta Amurka ta fuskanci fushin hukumar FIFA, domin kuwa hukumar ta hana gwamnati tsoma baki a cikin harkokin da suka shafi sha'anin kwallon kafa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel