Nigerian news All categories All tags
An bawa hammata iska tsakanin ma'aikata da 'yan kungiyar kwadago a filato

An bawa hammata iska tsakanin ma'aikata da 'yan kungiyar kwadago a filato

- Murnar ranar ma'aikata ta duniya a jahar Jos tazo da wani salo

- Mai'aikatan jihar sunyi ta ihu inda inda suke daga yatsu uku a sama a ke nuni da albashinsu na wattani uku da ba'a biyasu ba

- Wannan hayaniyar ya janyo an bawa hama iska tsakanin magoya bayan shugaban NLC da abokan hammayarsa

Murnar ranar ma'aikata a jihar Plateau ta rushe saboda musayar naushe-naushe da akayi tsakanin magoya bayan ciyaman din kungiyar kwadago (NLC) Jibrin Banchir da abokanan hamayyar sa.

An bawa hammata iska tsakaninma'aikata da 'yan kungiyar kwadago a filato

An bawa hammata iska tsakaninma'aikata da 'yan kungiyar kwadago a filato

Bayan tashi daga taron, jami'an 'Yan sandan farin kaya (DSS) sun rakoshi ya fito daga filin wasanni na Rwang Pam da akayi taron.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe wani hadimin gwamnan Najeriya

Kafin afkuwar lamarin kungiyoyi malamai da ma'aikata na Plateau yayin gabatar da fareti sun kasance kowannan su yana daga yatsu uku wanda hakan ke nuni da albashin su na watanni uku.

Banchir ya hau wajen yin magana amma ihun ma'aikata ya hana shi.

Rashin amincewar su ya zanjo wata hayaniya tsakanin magoya bayan NLC ciyaman da abokan hamayyar sa suka fara kaiwa juna naushi.

Duk da cewa Banchir yayi kokari farkon bashi ciyaman na NLC amma daga baya tauraruwar sa ta disashe bayan ya zama na kusa da tsohon gwamnan jahar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel