Nigerian news All categories All tags
Maka El-Zakzaky da gwamnatin Kaduna ta yi kotu abin takaici ne – Kungiya

Maka El-Zakzaky da gwamnatin Kaduna ta yi kotu abin takaici ne – Kungiya

Wata kungiya mai nemawa wadanda aka zalunta hakkinsu, mai suna Access to Justice, ta yi Allah wadai da Gwamnatin Jihar Kaduna.

Hakan ya biyo bayan maka shugaban mabiya Shi’a na Najeriya Ibrahim El-Zakzaky kotu da gwamnatin tayi.

Gwamnatin Kaduna ta shigar karar sa kotu inda aka zarge shi da laifuka guda takwas, ciki har da laifin kisa da aka ce ya afku a cikin watan Disamba, 2015, ranar da mabiyan sa suka yi hargitsi da sojoji a Zaria.

A hargitsin dai sojoji sun kashe mabiyan sa 348, yayin da soja daya ya rasa ran sa.

Fadan ya afku ne bayan da mabiyan malamin suka tare hanya, suka hana tawagar Shugaban Hafsoshin Sojan Kasar nan, Tukur Buratai wucewa.

Maka El-Zakzaky da gwamnatin Kaduna ta yi kotu abin takaici ne – Kungiya

Maka El-Zakzaky da gwamnatin Kaduna ta yi kotu abin takaici ne – Kungiya

“Irin yadda gwamnatin jihar Kaduna ta nuna rashin kunya da rashin sanin ya kamata, har ta ke neman hakkin soja daya da ya rasa ran sa, alhali ta kau da kai ga al’umma sama da 348, ta nuna rayukan su da ta kashe ba a bakin komai suke ba, hakan rashin tausayi ne, wulakanci ne, zunubi ne kuma bai yi daidai da kowace irin tafarkin dimokradiyya ba.”

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya sake yin tsokaci akan matasan Najeriya

Haka Daraktan kungiyar mai suna Joseph Otteh ya bayyana a jihar Lagas.

Ya ce shi bai ma taba ganin nuna bambanci, bangaranci da tozarta rayukan al’umma irin na wannan mataki da gwamnatin jihar Kaduna ta aikata ba.

Ya ci gaba da cewa abin fa abin firgitarwa ne kuma abin kyama.

A baya-bayan nan dai an sha arangama tsakanin yan sanda a mabiya kungiya Shi'a dake zanga-zanga domin a saki shugabansu a Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel