Nigerian news All categories All tags
Kudin Kamfen: APC ta kalubalanci jam'iyyar PDP ta kawo shaida

Kudin Kamfen: APC ta kalubalanci jam'iyyar PDP ta kawo shaida

- Jam'iyyar APC mai mulki ta kalubalanci babbar jam'iyyar ta PDP da tayi wa mutane bayanin kudaden ta idan har tana da wata kwakkwaran shaida

Kudin Kamfen: APC ta kalubalanci jam'iyyar PDP ta kawo shaida

Kudin Kamfen: APC ta kalubalanci jam'iyyar PDP ta kawo shaida

Jam'iyyar APC mai mulki ta kalubalanci babbar jam'iyyar ta PDP da tayi wa mutane bayanin kudaden ta idan har tana da wata kwakkwaran shaida.

DUBA WANNAN: Trump ya nemi goyon bayan Najeriya don basu bakuncin gasar cin kofin duniya na 2026

APC ta kalubalanci jam'iyyar hamayyar ne a jiya ta bakin sakataren hulda da jama'a na kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa APC dai bata ari halin PDP na satar kudin al'umma don daukar nauyin al'amuran jam'iyyar ba kamar dai yanda sukayi a zaben 2015.

Jam'iyyar ta APC tana maida martanin ne akan zargin da PDP take mata na tsarin da tayi na taronta na kasa a 2018.

Jam'iyyar PDP tace wai shugaban kasa ya tilasta gwamnonin da suyi amfani da kudin al'umma don daukar nauyin taron ta na shekara da ke gabatowa.

Amma gurin maida martanin a jiya, APC tana nufin bayanin kudin PDP ne na shekara 2016.

"Bayan haka ma, mun bayyana kudaden da zamu kashe na taron jam'iyyar na kasa da kuma zaben sababbin jami'ai na kasa a tsarin kashe kudin mu na shekarar 2018. Don haka maganar zamu kashe Naira biliyan 6 ba matsalarku bace."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel