Nigerian news All categories All tags
Rikicin Makiyaya: Na bada umarni a kara yawan Ma’aikatan ‘Yan Sanda – Buhari

Rikicin Makiyaya: Na bada umarni a kara yawan Ma’aikatan ‘Yan Sanda – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda yanzu yana Babban Birnin Kasar Amurka yace ya bada umarni a dauki sababbin Jami’an ‘Yan Sanda 6000. A hawan wannan Gwamnatin an dai dauki Ma’aikata 10000 na ‘Yan Sanda.

Shugaban kasar ya nemi a kara yawan ‘Yan Sanda ne domin kawo karshen rikicin Makiyaya da Manoma. Shugaba Buhari ya bayyana wannan ne lokacin da yayi magana da Gidan Rediyon VOA na Amurka a Ranar Talatar nan.

Rikicin Makiyaya: Na bada umarni a kara yawan Ma’aikatan ‘Yan Sanda – Buhari

Buhari yace a dauki sababbin ‘Yan Sanda aiki a Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari yace ya ba Hukumar ‘Yan Sanda dama ta nemo karin Jami’a 6000 daga kowace karamar Hukuma na fadin kasar. Buhari yace idan ta kama a dauki Ma’aikatan a Kananan Hukumomin su ne ayi hakan.

KU KARANTA: Ana sa rai Buhari ya amince da karin albashin Ma'aikata

A hirar da Shugaba Buhari yayi bai nuna amincewar sa da kirkiro Jami’an ‘Yan Sanda na Jihohi ba inda yace ya kamata a duba abin da tsarin mulki ya tanada da kuma kalubalen da ake samu wajen biyan albashi a wasu Jihohin kasar.

Kwanakin baya da aka yi kokarin daukar Ma’aikatan Hukumar shige-da-fice na kasar an samu rauni a dalilin yawan da aka yi wajen neman aikin. Buhari yayi bayani da dama wanda su ka hada da jawabin da yayi kan matasa kwanki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel