Buhari ya kunyata kasar Najeriya a ziyarar da ya kai Amurka - PDP

Buhari ya kunyata kasar Najeriya a ziyarar da ya kai Amurka - PDP

Jam'iyyar PDP ta soki ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai kasar Amurka.

Ta bayyana cewa Shugaba Buhari ya kunyata Najeriya a ziyarar, cewa ya kasa tallata kasarsa a gaban manyan jami'an gwamnatin Amurka.

Sakataren Jam'iyyar na kasa, Kolawale ya ce a lokacin tattaunawa da Shugaban Amurka, Donald Trump shugaba Buhari ya ki fitowa fili ya yiwa Amurka tayin ci gaba da sayen danyen man fetur da Najeriya ke samarwa bayan ta dakatar da sayen man.

Ya ce, a maimakon yin hakan, ya shaidawa Amurkawan cewa shi ba zai iya gayawa Amurka abin da za ta yi ba amma acewar PDP, Amurka ta fito ta gayawa Najeriya bukatunta.

Buhari ya kunyata kasar Najeriya a ziyarar da ya kai Amurka - PDP

Buhari ya kunyata kasar Najeriya a ziyarar da ya kai Amurka - PDP

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Donald Trump a ranar Litinin yace zaiso ya ziyarci Najeriya, bayan ya misalta ta a matayin kasa mai dadin ziyarta.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya sake yin tsokaci akan matasan Najeriya

Trump yace kamar yadda ya samu labari cewa Najeriya kasace mai kyau da dadin ziyarta wadda babu kamarta, ya bayyan haka ne lokacin da yake karbar bakuncin shugaba Buhari a fadar shugaban kasa a Amurka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel