Nigerian news All categories All tags
Kakakin Majalisa Dogara yayi wa Ma’aikatan Najeriya albishir

Kakakin Majalisa Dogara yayi wa Ma’aikatan Najeriya albishir

- An tado da maganar kara albashin Ma’aikatan Najeriya a Ranar kwadago

- Yakubu Dogara yace ana sa rai Buhari zai aiko masu kudirin kari albashin

- Shugaban Majalisar yace duk za su mara baya idan aka aiko masa kudirin

Majalisar Tarayya ta bayyana a shirya ta ke tayi iya abin da za ta iya domin ganin an kara albashin Ma’aikatan Najeriya idan an samu damar hakan. Kakakin Majalisar Kasar Yakubu Dogara ya bayyana wannan a Birnin Tarayya Abuja.

Kakakin Majalisa Dogara yayi wa Ma’aikatan Najeriya albishir

Shugaban kasa ya nada kwamiti domin duba batun karin albashi

Rt. Hon. Yakubu Dogara a wani jawabi da yayi ta bakin Mai ba shi shawara Mista Turaki Hassan ya bayyana cewa Majalisar Wakilan Tarayya a shirye ta ke tayi na’am da kudirin kara albashin Ma’aikata da zarar ya zo daga Shugaban kasa.

KU KARANTA: Gwamnan Jam'iyyar APC ya nemi gafarar Jama'a

Kakakin Majalisar ya nuna cewa ya san irin wahalar da ‘Yan kwadagon kasar ke sha yana mai cewa Majalisa na kokarin ganin an inganta jin dadi da rayuwar su. Dogara yayi wannan jawabi ne a 1 ga Watan Mayu watau Ranar kwadago ta Duniya.

Dogara ya kuma kara da cewa yana sa rai kwamitin da Buhari ta nada domin duba albashin Ma’aikata ta karkare aikin ta. Yanzu haka kwamitin na zagaye kaf Yankunan Kasar wanda bayan nan ana sa rai za a aikowa Majalisa kudirin karin albashi a Najeriya.

Shugaban Majalisar yace idan wannan kudiri ya zo hannun su daga fadar Shugaban kasa duk za su goyi bayan sa. Dama shi ma Ministan kwadago na kasa Dr. Chris Ngige yayi magana game da albashin Ma’aikatan yace Gwamnati na kallon lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel