Aisha ta koda Buhari yayin da yake Amurka, ta ce ya cancanci yabo da jinjina

Aisha ta koda Buhari yayin da yake Amurka, ta ce ya cancanci yabo da jinjina

Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta yabi mijin ta, shugaba Buhari, bisa yadda ya fito jiya yayin ganawa da shugaban kasar Amurka, Donald Trump.

Aisha Buhari tayi kalaman na yabo ga mijinta a shafin ta na Instagram, @aishambuhari.

A kasan kalaman da tayi ta saka wasu hotunan shugaba Buhari da takwaran sa na Amurka, Donald Trump.

A daya daga cikin hotunan, an ga shugaba Buhari cikin murmushi yayin da yake saka hannu kan wasu takardu, a bayan sa kuma shugaba Trump ne cikin murmushi ya dafa kujerar da Buhari ke zaune.

Aisha ta koda Buhari yayin da yake Amurka, ta ce ya cancanci yabo da jinjina

Aisha Buhari

A jiya ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da takwaran sa na kasar Amurka, Donald Trump, suka gana tare da yin jawabi ga manema labarai tare.

Ga wasu abubuwa biyar da shugaba Trump na Amurka ya fada yayin ganawar ta su

1. Shugaba Trump ya bayyana cewar baya nadamar kalaman sa a kan batun 'yan ci-rani daga Najeriya dake tururuwar zuwa Amurka da kuma wadanda suke can amma basa kaunar dawowa Najeriya.

2. Shugaba Trump ya musanta cewar sun yi tattauna da jami'an gwamnatin sa inda ya yi kalaman kaskanci ga nahiyar Afrika. Trump ya ce babu wannan maganar.

DUBA WANNAN: Majalisar dattijai ta zabtare farashin fom din takara, duba sabon farashin kowacce kujera

3. Trump ya bayyana cewar kwanannan Najeriya zata samu jiragen yaki na musamman da ta saya daga kasar Amurka da zarar an gama da duk wani batu dake da alaka da takunkumi daina sayar wa da Najeriya makamai da gwamnatin Obama ta kakabawa Najeriya, wanda kuma Trump ya janye shi.

4. "Ba zamu yarda da kisan Kiristoci ba a Najeriya," a cewar Trump. Trump ya ce kasar Amurka zata shiga maganar kashe mabiya addinin Kirista a Najeriya.

5. Shugaba Trump ya bayyana cewar yana ganin girma da kimar shugaba Buhari kuma zasu yi aiki tare domin inganta tsaro, kasuwanci, tattalin arziki da kuma kawo karshen kashe Kiristoci a Najeriya.

DUBA WANNAN: Ku yafe min idan nayi maku wani laifi - Gwamna Bindow ya nemi gafarar jam'iyyar APC

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel