Nigerian news All categories All tags
Murna baki har kunne: Amurka zata maidowa Najeriya $500m da aka sata

Murna baki har kunne: Amurka zata maidowa Najeriya $500m da aka sata

- Da alamu ziyarar shugaba Buhari tayo babban kamu

- Amurka ta yarda ta ingizo keyar wasu miliyoyin daloli da ka sace zuwa Najeriya

- Shugaba Buhari ne ya bayyana haka yayin ziyarar aiki da yakai Amurkan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, kasar Amurka zata maidowa da Najeriya zunzurutun kudaden da aka sata aka jibge cikin asusun ajiya da suka kai $500m.

Muhammadu Buhari ya fadi hakan ne a jiya Litinin, yayin ganawa da yan jarida tare da shugaban kasar Amurkan Donal Trump bayan tattaunawarsu a fadar White House.

Murna baki har kunne: Amurka zata maidowa Najeriya $500m da aka sata

Murna baki har kunne: Amurka zata maidowa Najeriya $500m da aka sata

KU KARANTA: Hankali kwance Buhari zai lashe zaben 2019 Inji Festus Keyamo

Buhari ya ce, kudaden an dai ajiye su ne a bankuna daban-daban na duniya.

Ya ce, “Mun cimma kudirin yi aike tare domin baiwa hukumomin shari’ar kasashenmu dama wajen hadaka don dawo da kudaden Najeriyar da suka kai $500m gida”

Shugaba Buharin ya kuma ce, “A yayin tattaunawarsu da shugaba Trump din, sun tattauna batutuwan da suka shafi tsaro da tattalin arziki da kasuwanci da hakkin dan Adam.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel