Nigerian news All categories All tags
EFCC ta gano cewa wani Ministan Jonathan ya wawuri kusan Biliyan 4

EFCC ta gano cewa wani Ministan Jonathan ya wawuri kusan Biliyan 4

- Hukumar EFCC na binciken wani tsohon Ministan sufurin jirgin sama

- Ana dai zargin Osita Chidoka ya saci wasu Biliyan 3.9 lokacin yana ofis

- Tsohon Ministan dai ya mika kan sa a gaban EFCC ya amsa tambayoyi

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta yi ram da tsohon Ministan sufurin jirgin sama Osita Chidoka game da wasu makudan kudi da ake zargin sa da yin gaba da su.

EFCC ta gano cewa wani Ministan Jonathan ya wawuri kusan Biliyan 4

Ministan sufurin jirgin sama Mista Osita Chidoka

Hukumar ta EFCC na zargin cewa Osita Chidoka ya saci wasu kudi da su ka kai Naira Biliyan 3.9. An zari wannan kudi ne da sunan za a sanya na’u’rorin inganta tsaro rin su kemarar hoto a manyan filayen jirgin saman kasar 5 da ake da su.

KU KARANTA: Maganar tsige Shugaba Buhari ba za ta kai ko ina ba

A Jiya Litinin da rana ne Chidoka ya bayyana gaban EFCC a ofishin su ne Legas inda ya sha tambayoyi. An rahoto dama tuni an damke Shugabannin Kamfanin Bri and Bru da kuma wasu manyan Darektoci a Hukumar FAAN.

Binciken EFCC ya nuna cewa an biya wasu kudin wannan kwangila da aka bada na daura na’urori a filayen jirgi a asusun Osita Chidoka. An kuma aika wasu kudin ne zuwa akwatin bankin Obinna Chidoka wanda ‘Dan uwan Ministan ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel