Nigerian news All categories All tags
Karin albashin Ma’aikatan Najeriya yana gaban ShugabaBuhari – Minista

Karin albashin Ma’aikatan Najeriya yana gaban ShugabaBuhari – Minista

Ministan kwadago na kasa Chris Ngige yayi magana game da albashin Ma’aikata a Najeriya inda yace Shugaban kasar ya damu da lamarin da ke kasa ya kuma yi kira a cigaba da goyon bayan wannan Gwamnati ta Shugaba Buhari.

Dr. Chris Ngige ta bakin Darektan yada labaran Ma’aikatar sa Samuel Olowookere ta bayyana cewa Gwamnatin Buhari tana da tanadi game da albashin Ma’aikata a kasar. Ministan yayi wannan jawabi ne domin wannna rana ta kwadago.

Karin albashin Ma’aikatan Najeriya yana gaban ShugabaBuhari – Minista

Ministan kwadago Ngige ya aikawa Ma'aikata jawabi

Ngige yace Gwamnatin Tarayya na kokarin samawa kowa aikin yi a kasar, a dalilin haka ne ma Ministan yace tun da Gwamnatin Buhari ta hau mulki babu wanda aka sallama daga ofis duk da matslar kuwa da aka shiga na tattalin arziki.

KU KARANTA: An damke wani 'Dan takarar Gwamna a Najeriya

Manema labarai sun rahoto cewa Ministan kasar yayi kira ga ‘Yan kwadagon su yi amfani da wannan rana da Ma’aikata ta hanyar da ta fi dacewa. Yanzu haka dai kun san cewa ana zama domin ganin an kara albashin Ma’aikatan Najeriya.

Ngige yace kwamitin da Shugaba Buhari ya kafa ta duba albashin Ma’aikatar ya isa ya zama shaida cewa da gaske Gwamnatin nan ta ke wajen kula da jin dadin Ma’aikatan Najeriya. Tattalin arziki dai na cikin alkawuran da Buhari yayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel