Nigerian news All categories All tags
Amurka zata dawo ma Najeriya da zambar kudi dala miliyan 500 – Buhari

Amurka zata dawo ma Najeriya da zambar kudi dala miliyan 500 – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin kasar Najeriya da ta Amurka sun shiga wata hadin gwiwa don ganin sun kwato ma Najeriya zambar kudi naira miliyan dar biyar, $500m, kudin jama’a da aka sace daga Najeriya, inji rahoton Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya sanar da haka ne a ranar Litinin 30 ga watan Afrilu a yayin wata tattaunawa da yan jaridu da yayi tare da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, bayan ganawar sirri da suka yi a fadar gwamnatin Amurka, White House.

KU KARANTA: Manyan jiragen ruwa guda 32 dauke da man fetir da kayan abinci na gab da isowa Najeriya

Buhari yace an sace kudaden ne daga Najeriya, inda aka jibgesu a bankuna da dama dake fadin Duniya: “Gwamnatocinmu sun dauki matakan kwato ma Najeriya dala miliyan 500 kudaden Najeriya da aka sata dake jibge a bakuna da dama ta hannun ministocin shari’un kasashen biyu.

Amurka zata dawo ma Najeriya da zambar kudi dala miliyan 500 – Buhari

Trump da Buhari

“Da wannan ne muke taya kasar Amurka murna tare da yin maraba da kafa kwamitin kwato kudaden sata, wanda ma’aikatan shari’a ta kasar Amurka ke jagoranta, muna fatan zamu cigaba da samun goyon bayan Amurka ta wannan bangare” Inji Buhari.

Daga karshe Buhari yace sun tattauna batun kare hakkin bil adama, tsaro, zuba hannayen jari, kasuwanci, sha’anin mulki da kuma matsalolin yan gudun hijir da shugaba Trump.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel