Nigerian news All categories All tags
Gwamna Yahaya Bello ya juyawa jami’ansa baya sakamakon gazawarsu na yiwa Sanata Melaye kiranye

Gwamna Yahaya Bello ya juyawa jami’ansa baya sakamakon gazawarsu na yiwa Sanata Melaye kiranye

- Gwamnan jihar Kogi ya yanke shawarar korar wasu daga cikin jami’ansa sakamakon gazawarsu wurin yiwa Sanata Melaye mai wakiltar kogi ta yamma kiranye

- Gwamnan bai dauki lamarin yiwa sanata Melaye kiranye abun wasa ba, kuma yayi barazanar korar wasu daga cikin jami’an nasa ko kuma ya dakatar dasu har sai sun myar da kudaden da aka biyasu don yiwa sanatan kiranye

- Hakan na faruwa ne duk da cewa gwamnatin jihar tace bata wata alaka da kiranyen da ake yunkurin yiwa sanatan

Gwamnan jihar Kogi ya yanke shawarar korar wasu daga cikin jami’ansa sakamakon gazawarsu wurin yiwa Sanata Melaye mai wakiltar kogi ta yamma kiranye.

Majiya ta kusa da Bello ta bayyana cewa, Gwamnan bai dauki lamarin yiwa sanata Melaye kiranye abun wasa ba, kuma yayi barazanar korar wasu daga cikin jami’an nasa ko kuma ya dakatar dasu har sai sun mayar da kudaden da aka biyasu don yiwa sanatan kiranye.

Hakan na faruwa ne duk da cewa gwamnatin jihar tace bata wata alaka da lamarin kiranyen da ake yunkurin yiwa sanatan.

Gwamna Yahaya Bello ya juyawa jami’ansa baya sakamakon gazawarsu na yiwa Sanata Melaye kiranye

Gwamna Yahaya Bello ya juyawa jami’ansa baya sakamakon gazawarsu na yiwa Sanata Melaye kiranye

Jami’an gwamnan 555 da ya nada daga karamar hukumar Kabba wadanda suka kasa samar da sanya hannun mutane sama da 2085 don yiwa sanatan kiranye, suna cikin wadanda gwamnantin zai juya kansu.

KU KARANTA KUMA: Zan so na kawo ziyarar ban girma Najeriya - Inji Trump

Akwai kananan hukumomi bakwai dake kan gaba wurin lamarin yiwa sanata kiranye. Majiya ta bayyan cewa N200,000 aka raba a mazabobi 552 inda ake kokarin hada sanya hannun mutane domin cimma nasarar adadin da ake bukata don yiwa sanatan kiranye, wanda jami’an nasa ne aka bawa hakkin kula da wuraren.

A karshen makon da ya gabata ne hukumar zabe mai zaman kanta ta shirya yiwa Sanata Dino kiranye sai dai hakan bai yiwu ba domin shi yayi nasara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel